Connect with us

SIYASA

Kofa A Bude Ta Ke Ga Duk Wanda Ke Sha’awar Canja Sheka –ADP

Published

on


Sabuwar jam’iyyar ADP ta bayyana cewar halin kunci da rashin cika alkawurra daga jam’iyya mai mulki ya ba ta damar samun kwarjini a wajen al’umma, wanda a cewarta duk da cewar jam’iyyarsu sabuwar jam’iyya ce amma ko wace rana tana samun baki masu sha’awar shigowa, shugaban jam’iyyar a jihar Neja, Kwamared Jamilu Sarki Kwamba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a minna, yace yanzu haka a dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar da ke jihar ba inda jam’iyyar ba ta samun baki, wanda hakan na kara daga darajar jam’iyyar a siyasance.

Kwamared Kwamba yace ADP ce kadai ke da tsarin duk wani dan jam’iyya mai rajista dalaget ne, domin a lokacin zaben shugabannin jam’iyya da na ‘yan takara mun tsara a cikin dokokin jam’iyya duk wani mamba mai rajista daga mazabe har kananan hukumomi dalaget ne kuma ko wani zabe a nan mazabar unguwa za a tabbatar an yi shi.

Akidar ADP ba bambamci domin mutumin da ya shigo cikin jam’iyya yau dai-dai yake da wanda ya faro jigilar kafa ta, ko yau ka shigo indai za ka aiki da dokokin jam’iyya kana daidai da kowa ne kuma kana iya neman kowace irin matsayi, babban abin bukata shi ne ka nemi amincewar jama’ar yankin ka, indai mazabar ka ta amince da kai to duk abinda za a yi a jam’iyyance da kai za a yi. Duk wanda yazo a sakatariyar jiha neman abu, za mu tura shi zuwa ga shugaba na karamar hukuma ne, shi kuma shugaban karamar hukuma zai tura shi zuwa mazaba ne, babban bukatar ADP a yi siyasa na gaskiya ba tare da murdiya ko dan ne hakki ba.

Mun sani jam’iyyu guda biyu muke su a kasar nan yau, ADP da sauran jam’iyyu amma tsarin mu ya bambamta da sauran tsarin jam’iyyun siyasa a kasar nan, mune kadai keda tsarin tantance ‘yan takara ta hanyar anfani da kuri’un ‘yayan jam’iyya ba dalaget ba, dan haka ba na kokwanto 2019 in har ana neman tabbatar da siyasa ta gaskiya, siyasar da za a baiwa jama’a damar kare hakkinsu to ADP za a yi.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai