Connect with us

SIYASA

Ba Zan Zabi Buhari A 2019 Ba –Dakta Junaid

Published

on


Dakta Junaid Mohammed sanannen dan siyasa ne kuma mai yin fashin baki akan alamuran kasa, ya kuma taba zama dan majalisa a jamhuriyya ta biyu.

A hirarsa da Abubakar Abba a Kaduna Dakta Junaid ya yi akan gwamnatin shugaba Buhari, musamman akan tazarcen da Buhari yake son yi a shekarar 2019 da maganar yaki da cin  hanci da rashawa da sauransu. Ga yadda hirar ta kaya:

Zaben 2019 na kara karatowa, shin Arewa ta gamsu da kamun ludayin shugabancin Buhari kuma zaku sake zabarsa karo na biyu?

Da farko dai in har zanyi zabe a shekarar 2019, ni inda da kuri’a daya ce kuma ba zan iya garantin kuri’ar mata ta da yara na ba, saboda suma suna da nasu ‘yancin na jefa kuri’ar a asirce ba tare da sun sanar dani wanda suka zaba ba.

Duk da haka nayi amana cewar, mulkin dimokiradiyya wata cibiyace murdaddiya kuma nayi amana da cewar babu wani shugaba da zai wakilci kansa a zabe ko kuma a sake zabarsa, sai in har yanada kwararan dalilai da zai sake jan ra’ayin wadanda zasu zabe shi cewar a zai iya da kuma cewar shugabancin shi zai amfani kasa kuma jama’a sun aminta dashi da kuma waye zai iya.

Toh a bisa wadannan dalilan, ni Buhari bai ji nawa ra’ayin ba na ya kara mika kansa don a sake zabarsa a shekarar 2019 ba.

Sai dai baza a iya saurin cewa ba zai iya wata hobbasa ba, wajen samar da wani abu mai kyau ba a kasar, kamar yadda yasha yin alkawura a wasu tarurruka, amma a yanzu dai in babu ci gaba, koda yake ni bana hangen cewar akwai wani ci gaba, amma, zan iya cewa ni dai kam, banga wani abu da Buhari ya yi ba tunda ya dare karagar mulkin kasar nan a shekarar   2015 ba kuma bansan wasu abin mamakin da zai mikawa ‘yan kasa  a shekarar 2018 ba, daga watan Janairu zuwa watan Maris na shekarar 2019, lokacin ne za’a fara shiga maganar yi zabe.

 

Amma kana ganin ‘yan Arewa zasu sake zabar shi a 2019 ?

A iya sani na, mutane masu ra’ayi zasu yanke hukuncin da zasu yanke har zuwa wani lokaci na karshe, don suyi adalci a gare shi da jamiyyar sa da kuma wadanda yake wakilta.

Amma sai dai abin bakin ciki, idan ka kalli mutanen dake zagaye dashi, wadancan da yake ta kokarin ya kare domin kamar ba kowa yake wakilta ba, domin wadanda suke zagayen dashi ba ‘yan Nijeriya suke wakilta ba.

A iya sani na, mutane masu ra’ayi zasu bar hukuncin da zasu yanke har zuwa wani lokaci na karshe, don suyi adalci a gare shi da jamiyyar sa da kuma wadanda yake wakilta.

Amma sai dai abin bakin ciki, idan ka kalli mutanen zagaye dashi, wadancan da yake ta kokarin ya kare domin kamar ba kowa yake wakilta ba, domin wadanda suke zagayen dashi, ‘yan Nijeriya suke wakilta ba.

Ministoci kamar Babatunde Fashola da sauran su da suke ta kai komo suna fakewa a matsayin kare masa muradun sa ne, amma a hakikanin gaskiya suna yi masa zagon kasa ne, don ganin cewar dukkan wasu manyan ayyuka an kaisu yankunan da suka fito don wata ajandar su da suke da ita amma ba wai don amfanin ainahin mutanen da suka zabi Buhari ba, suna kawai zagaye jama’ar da suka zabe shi ne.

Babu wata maganar gaskiya dukkan abubuwan da suke faruwa tun daga shekarar 2015 har zuwa yau, babu wani   mutum da zaice wadannan su ne dalilai da zai sake zabar wannan mutumin.

A yanzu akwai wasu mutane da suke yawo, wanda wannan wani kamfen ne na wata manufa dake yawo a tsakanin wasu ‘yan hana ruwa gudu na mambobin iyalisa da kuma wadanda suke zagaye dashi, inda suke yin amfani da wasu sarakunan gargajiya da wasu kabilu da kuma yin amfani da addinni.

Abin da suke cewa a yanzu shine, saboda shi dan Arewa ne dole na ‘yan Arewa su sake zabar sa. Ni dan Arewa ne   Musulmi amma ba zan zabe shi ba kuma akwai ‘yan Arewa da yawa da baza su zabe shi ba.

Tunda ya dare karagar mulki, sun karbi biliyoyn naira ko tirliyan da suke son su murda zabe ko su tayarda tarzoma a ranar zabe ko kuma su sa a dinga kama jama’a ba gaira ba sabat, kuma irin hakan ne ya yi lokacin da yake shugaban kasa na soja daga shekarar 1984 zuwa watan Agustan shekarar 1985, idan ya yi hakan, kasar  zata fada a cikin ruduni, kuma bana jin zai iya jurewa rudanin da zai tashi a kasar saboda dama ta tabbata a zahiri a zake yake na son sai ya zama shugaban kasa.

Wani abin takaici ga kasar nan, wadanda suke son su gaje shi a cikin APC ko PDP ko a tsakanin wayanncan ‘yan jeka nayi ka ‘yan Arewa, duk suma a zake sun kagara su gaje shi.

Saboda haka APC a zake take haka PDP kuma mutane kamar irin su Atiku Abubakar da sauran, suma duk a zake suke, toh kaga haka abin yake, akwai abubuwa da dama wadanda zasu iya jefa kasar a cikin rudani in ba’a yi hankali ba kuma na damu matuka akan hakan.

Ko wanene zai  shugabancin kasar ba abin da ya dada shi da kasa, kuma duk wannan Nijeriya abin zai shafa, kuma Buhari baiyi mana abin da ya dace ba a zaman mu na mutane harda ita  APC a matsayin jamiyya, wadanda suke zagaye da dangen sa da abokansa sune kawai ‘yan lele.

Ina kalubalantar  wadanda zasu fito da kuma wadanda a yanzu suke cewa mu zabi Buhari dasu gaya mana wanne aiki ne Buhari ya yi har da za’a sake zabarsa.

 

Kana nufin baka gamsu da yadda yake yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da ‘yan ta’adda ba?

Maganar a bayyane take akwai badakala akan yaki da ‘yan ta’addacin da gwamnatin take yi, sabanin akan abin da yake cewa, domin ‘yan Boko Haram sai kara fitowa suke yi har suna kara zama barazana a duniya.

Babu kuma wanda zai iya gaya mini cewar wannan gwamnatin taci nasara akan yakin da take yi da ‘yan Boko Haram, abin da ya fada a jawabinsa ga ‘yan Nijeriya a ranar sabuwar shekara, hakan ya nuna a zahiri, bashi ne akan lamarin a Arewa Maso Gabas ba.

Sauran irin hare-haren dake aukuwa a yankin Neja Delta ba wai lallai suna karkashin kulawa bane, abin da yake ci gaba da yi shine bawa ‘yan tsagerun cin hanci don su daina tayar da kayar baya har zuwa bayan zabe.

Sannan kuma idan ka dubi yaki da cin hanci da rashawa shima duk a cikin rudu ake yin sa saboda abin da ke faruwa shine, ‘yan hana ruwa dake zagaye dashi da sauran wadanda ya nada, sune suke yiwa yaki da cin hancin da rashawa zagon kasa.

Babbar barazanar itace, Ibrahim Magu ayau sune mutanen da suke cikin APC jamiyyar Buhari kuma wasu mutanen da ya dora kamar Darakta Janar na SSS da sauran mutane wadanda a yanzu suke yin zagon kasa suke son su bata yakin da ake yi na cin hanci da rashawa, kuma mafi yawancin mutanen da suke fitowa basa tabuwa domin su ‘yayan jamiyyar sa ne kuma sune ke rike da madafun iko a cikin gwamnatin Buhari.

Sannan kuma idan ka kalli yarda ake tafiyar da tattalin arzikin koda yake bai kirkiri wasu sharudda na hana yiwa tattalin arzikin kasa almundahana ba, amma dole ne a amince akan rashin fahimtar sa akan tattalin arzikin kasa ba duk hakan ya kara janyo jefa kasar cikin radadin arzikin kasa wanda za’a dauki tsawon lokaci kafin kasar ta fita daga cikin sa.

Saboda haka wannan sune matsalolin da ake magana akai, na dauka cewar zamu ga alfanun wannan sabuwar gwamnatin,  amma bamu gani ba, kuma babu wani alamu da ke nuna cewar za’a iya tafiyar da tattalin arzikin Nijeriya nan da watanni sha biyu ko sha biyar masu zuwa ba, alhali

zabe ya riga yazo.

Wannan shine tunani na na kashin kaina kuma a shirye nake in fuskanci ko wanene, haka ko wanene zai kalubalance ni  saboda abin da nake fada inada hujjoji ba wai maganar addini bane ko kabilanci ko adawa ba.

Ya mamaye mu akan maganar ministoci, domin abin a bayyane yake tun a rana ta farko, nayi tir da nade-naden da ya yi misali nadin Sakataren Gwamnatin Tarayya wanda aka kora na danganta shi a matsayin mai almubazzari kuma sai gashi hakan ta tabbata haka na yi magana akan Shugaban Ma’aikata na tarayya wanda nace shima almubazzari ne kuma ba mutumim da za’a dogara akansa bane, shima hakan ya tabbata.

Na kuma fada cewar mafi yawancin mutanen da aka nada ministoci, dukkan su Mamman Daura da sauran mambobi na Kaduna Mafiya sune suka shigo dasu a cikin gwamnatin, kuma wannan maganar tawa itama ta tabbata, kuma a yanzu sune suke  zama manyan  barazana a sake zabar Buhari, saboda basu tabuka komai ba, sauran suma duk basu da wani amfani haka ofishin Atoni Janar nan ma wata matsalar ce, kuma a yanzu Buhari har ya fara wuce makadi da rawa saboda fara kamfen da ya yi, ka kalli bayanin sa na sabuwar shekara nan, wanda mutane marasa tunani suka  rubuta masa, duk abin da yake fada maganar zaben shi ce, babu wani aiki da ya yi ikirarin zai fara alal misali, maganar aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano a haka ake tafiyar da ita.

Kuma maganar sa ta sada babban biranen jihohi da layin jirgin kasa, ban san yadda  za’a iya yin wannan aikin ba kuma ban san wacce dabara ce za’a yi ba da a yanzu yake magana akai, domin idan baka da wata dabara mai kyau akan aikin titin Kudu Maso Yamma daga jihar Legas zuwa Kalaba da wani aikin hanyar jirgin kasa daga Legas zuwa Kalaba, shin wanne irin kaya ne  za’a yi dakon su? saboda Legas a gefen teku take haka  Kalaba ma, to wanne irin kaya ne za’a yi jigilarsu? babu wani abu, kuma yanzu muna cik.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai