Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ba Za ta Iya Kamo Barcelona Ba -PUYOL

Published

on


Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Cales Puyol ya bayyana cewa abune mai wahala kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta iya kamo tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona akan teburin laliga na kasar

Barcelona ta bai wa Real Madrid mai rike da kofin La Liga tazarar maki 16, bayan da aka buga wasannin mako na 18 wanda hakan kuma yasa kungiyar wadda Zidane yake jagoranta take mataki na hudu a yanzu

A ranar Lahadi kungiyoyin biyu suka buga wasannin mako na 18, inda Barcelona ta doke Lebante da ci 3-0, ita kuwa Real Madrid 2-2 ta yi da Celta Bigo a gidan Celta Bigo din.

Barcelona ta ci gaba da zama a kan teburin La Liga da maki 48, ita kuwa Real mai kwantan wasa daya tana ta hudu da maki 32 yayinda kungiyoyin Balencia da Atletico Madrid suke gabanta.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Billareal a gasar mako na 19 a ranar 13 ga watan Janairu, inda Barcelona za ta ziyarci Real Sociedad a ranar 14 ga watan wanda kuma wasa ne mai zafi ga kungiyar ta Barcelona.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai