Connect with us

WASANNI

Neymar Da Messi Da Harry Kane Sun fi Kowanne Dan Wasa Daraja A Duniya

Published

on


Rahoton wani sabon bincike da masu bibiyar kwallon kafa suka yi na kasa da kasa a karkashin kungiyar CIES, ya nuna cewa dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane, shi ne dan wasa na uku mafi daraja a duniya.

Rahoton ya ce, a yanzu darajar Kane ta kai Euro miliyan 194. Hakan ya bashi damar zama mafi tsada ko darajar bayan dan wasan kungiyar PSG Neymar kan 213, da kuma Lionel Messi na Barcelona kan yuro miliyan  202.

An dai kafa ginshikan wannan bincike ne ta hanyar la’akari da darajar ‘yan wasan, a kungiyoyinsu na nahiyar turai bisa matakan shekaru, kwarewa, tsawon yarjejeniyar da suka sanyawa kungiyoyinsu hannu da kuma kimar ‘yan wasan a kasashensu.

A shekarar da ta gabata, Harry Kane ya samu nasarar cin kwallaye 56, a wasannin da ya bugawa kungiyarsa ta Tottenham da kuma kasarsa Ingila, hakan ya bashi damar zama dan wasan da ya fi kowa yawan kwallaye a nahiyar Turai.

Sauran ‘yan wasan da kungiyar sa idon ta CIES ta fitar da matsayin darajarsu a fagen na kwallon kafa, sun hada da Kylian Mbappe na PSG a matsayi na 4 kan euro miliyan 192.5, sai kuma Paulo Dybala na kungiyar Jubentus a matsayi na 5, kan yuro miliyan 174.6.

Dele Alli na Tottenham shi ne dan wasa na 6 mafi daraja kan yuro miliyan 171.3, sai kuma Kebin de Bruyne na kungiyar Machester City a matsayi na 7, kan yuro miliyan 167.8.

Binciken kungiyar ta CIES, ya nuna dan wasa na 8 mafi daraja shi ne Romelu Lukaku na Manchester United kan yuro miliyan 164.8, shi kuwa Antonie Griezman na Atlectico Madrid na a matsayi na 9 kan euro miliyan 150.2.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai