Connect with us

KASUWANCI

An Nada Alhaji Dan Lami Baban Joda Sarkin Fawan Jihar Filato

Published

on


Masu iya managa na cewa zakaran da Allah ya nufeshi da yin shara ko ana muzuru ana  Shaho, sai yayi, tabbacin wannan Karin maganan ya auku ne a juma’ar makon da ya gabata a lokacin da masu unguwannin dake cikin karamar hukumar Jos ta Arewa, da ke aiki a karkashin majalisar sarakuna na jihar Filato, suka hadu a babbar masallacin Jumma’a, na garin Jos, cibiyar gwamnatin jihar Filato, suka danka wa Alhaji Dan Lami Idi Baban Joda, mukamin Sarkin Fawan jihar Filato, bayan an dauki tsawon shekara Ashirin-da Hudu, ana kai kawo akan wa zai hau kujerar mulkin sarkin fawan jihar bayan rasuwar Sarkin Fawar jihar Marigayi Alhaji Inuwa Kure.

Alhaji Danlami Baban Joda, dan shekara 74, da haifuwa alokacin rasuwar marigayi Alhaji Inuwa Kure, shugaban majalisar sarakuna na jihar Filato kuma Sarkin Jos Marigayi Dr. Fom-Bot ya tabbatar da nadinsa, a wannan lakaci amma sai aka sami sabani sakanin ya’yan kungiyar ma’hauta na jihar akan waye ya can-canta ya gaji sarkin fawan sakanin shi Alhaji dan Lami da ya’yan marigayin wanda ta kaddamar yayi ta ja har Allah ya karbi rayuwar Dr. Fom-Bot, bayan an nada sabon sarkin Jos, Mr.  Bictor Pam, shima yazo yayi kokarin tabbatar masa da sarautar amma shima bai shi nasaraba har shima Allah ya karbi ransa, sai awannan lokaci akarkshin shugabancin mai-martaba, Da’ Jacob Gyang Buba, da Allah cikin rahamarsa yasa masu fada aji a jihar da masu ruwa da saki acikin harkar gudanar da sarauta a jihar suka ga yakamata su tabbatarmas kuma abokin hamayyarsa a takarar yazama ma taimakinsa.

Da yake Magana amadadin masu unguwannin da ke cikin garin Jos da kewaye abukin mika masa takardar kama aikin wanda shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa da Sakarensa suka sanya wa hannu, mai martaba Sarkin Narguta Injiniya Muhammad Bello, ya hori sabon sarkin da ya ribanya kokarinsa wajen yin aikin tukuru wajen cigaban kungiyar a jihar da kasa bakidaya kuma ya nemi ya’yan kungiyar da su bashi cikakken hadin kai da goyon baya don ya sami karfin guiwar tafiyarda harkokin kungiyar cikin nasara.

Da yake Magana da wakilimmu jim kadan bayan an mika masa takardar shaidar kama aiki, a matsayin sarkin fawan jihar Filato Alhaji Dan Lami Baban –Joda, yace ranar Jumma’a, 30, ga watan Disamba 2017 ranace na farin ciki wanda ba zai taba mantawa dashi ba a arayuwarsa.

Alhaji Danlami Idi Baban Joda, cike da farin ciki ya shaidawa wa kilimmu cewa ya’yafewa duk wandanda suka  so kawo cikas wajen nadin nasa kuma ya nemisu dasu yafe masa idan har yayi masu ba dai dai ba kuma yace ya yi imani Allah ne ke bada mulki wa mutum, alokacinda yaso.

Hakanan sabon sarkin Fawan yayi alkawarin yin aiki tukuru batare da nuna son kai ko bambanci ba wajen war-ware, dimbin mas’alolin dake damunsu kuma ya gode wa Gwamnan jihar da masu ruwa da saki akan harkar shugabanci a jihar kuma yayi addu’a, wa Allah da ya kara basu basirar gudanar da harkokin jagorancin jihar a cikin nasara.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai