Connect with us

SIYASA

Mu Ne ‘Yan Majalisar Da Suka Fi Kowacce Majalisa Yawan Dokoki A Cikin Shekara Biyu –Sani Zorro

Published

on


Kwamared kuma Honarabul MUHAMMAD SANI ZORRO, tsohon shugaban kungiyar ‘yan jaridu na kasa a shekaru sama da 20 da suka wuce, wanda ya tsunduma harkar siyasa da kafar dama.Shi ne Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kananna Hukomomi hudu na masarautar Gumel a Jihar Jigawa, a bayanin da ya yi kan rawar da suka taka a majalisa, da kuma gwagwarmayarsu ta tabbatar da ‘yancin‘yan Nijeriya, da kuma yadda wasu Janar-janar ake tuhunar su da keta haddin bil’adama aka hana su bizar kasashen Turai.

Sai kuma kutunguila da munafincin wasu Gwamnoni da suke kokarin tarwatsa Jam’iyarsu ta APC da sunan ba da tikitin kai tsaye ga Shugaban Kasa, da wasu ‘yan majalisu a matakin tarayya da na Jiha, inda kuma yayi sukuwa da zamiya a kan sabanin manufofin APC da Buhari da ya ce Gwamnan nasu ya sauka akan akidar Jam’iyar, da dai sauran bayanai da ya bayyana wa wakilinmu MUSTAPHA IBRAHIM Kano, Ga yadda ta kaya.

Honorabul za mu ce ko Kwamared a gabatar da suna da kuma matsayi?

Sunana muhammed sani zoro, kuma ni ne dan majalisa ne mai wakiltar kananan hukumomi hudu, wato Mai Gatari, Sule Tankarkar, Gagarawa, da kuma karamar hukumar Gumal ka ga masarautar Gumal ke nan dake jihar Jigawa. Haka kuma ni ne shugaban kwamitin lura da ‘yan gudun hijira na waje da na cikin gida, wato na Arewa maso Gabashin jahohin da ‘yan Boko Haram suka dai-daita a yaki na shekara takwas zuwa tara a wadannan jihohi dake nan Najeriaya.

Kamar jiya ne muke cikin shekarar 2017, yanzu kuma ne sabuwar shekarar 2018 ta fara, wacce nasara aka samu a Majalisar Wakilai da kake a can?

Koda yake ni ba mai magana da yawun Majalisa bane duk da na taba rike mukamin Shugaban kwamitin makogoran Majalisar na rikon kwarya, amma a gurguje ba wani abu ne mai wahala in fada ba, wasu nasarorin ba domin a kwanaki da muka yi bikin cikar shekaru biyu a wannan Majalisa ta Takwas mun yi dokoki sama da 100, kuma in ka yi la’akari da cewa aikin dan Majalisar dokoki, za kaga cewa ba karamar nasara bace, domin tunda ake Dimukradiyya bata taba samun Majalisar da ta yi aiki irin wannan ba, nasara ta farko ke nan.

Sai kuma abu na biyu shi ne, mun samu karbar korafe-korafe daga kungiyoyi ma’aikata kamar su NLC da sauran irinsu, wanda mun taka rawa wajen tsaida yajin aikin Ma’aikata da dai wasu al’amura kamar yajin aikin likitoci da wasu abubuwa na sasanta kungiyoyi da al’umma, da Gwamnati akan al’amuran da suka shafi cigaban kasa ta kowannan fanni a wannan lokaci na mu a Majalisa.

sai kuma kudure-kudure masu yawa a majalisa na jawo hankalin Gwamnati akan wasu abubuwa da za su taimaka wa al’umma wajen ci gabansu duk da kasancewar shi kuduri bai kai daraja ko mahimmancin dokoki ba, amma duk da haka ana yinsa domin samun wata masalahar al’umma. Bayan wannan kuma, a kullum sai mun bi diddigi akan abinda aka yi jiya a majalisa, wanda ko da tari ka yi sai an rubuta in an zo bin digdigi sai an duba a ga ina a kai kuskure a gyara, sannan in Shugaban Majalisa ya sa hannu shi ke nan sai a dora abinda za’ayi yau wannan duk aiki ne da mu ke yi.

Kwamitoci nawa kuke da su a Majalisa?

To akwai kwamitoci kamar 93 a majalisar wakilai da mu ke ciki, kuma su ne suke da alhakin duk wani abu da ya shafi tafi da al’amuran hokumomi da ake da su a Nijeriya, kamar kwamitin kula da harkar wutar lanatarki da duk wani abu da yake da alaka da ita. Sai kuma iskar gas da sauransu, haka akwai na ilimi, da na lafiya, da na matasa, da na wasanni, ga sunan har 93 ko wanne yana kan aikin da aka dora masa.

Baya ga wannan kuma kullum muna karbar korafi daga masu zanga-zanga idan sun zo su na zanga-zanga akan tura musu wakilai daga majalisarmu su karbi koke- kokensu a rubuce kan abinda ya fito da su har suke wannan zanga-zanga, kuma in mun zo majalisa bayan an yi addu’a irin tamu ta majalisa to kuma sai a tambayi korafe-korafen da aka samu a jiya tsakanin wani da wani ko wani ya kai kuka a mazabar wani na an zalunce shi ta hanyar korar aiki, ko an hana shi hakkinsa, ko kuma misali wasu manoma sun kawo kuka daga Gagarawa wani mai suna mr. lee dan kasar Caina ma zaunin Kano mai kamfanin takalma ya na son ya kwace masu gonaki kadada sama da 12,000, wanda yin haka ya saba ka’idar Nijeriya, domin a Caina ba za a ba wa dan Nijeriya ko kashi daya cikin goma ba, shi ma mr. lee din a Caina ba za’a ba shi ba, duk dai irin wadannan sai an bi diddigi na ganin mai kuka majalisa ta share masa hawaye akan kukan da ya kawo mata.

don haka ina ganin ‘yan Nijeriya ba sa amfani da damarsu yadda ya kamata su yi na kai kukansu majalisa ba, domin muna gani a kasashen turai kamar Ingila, a kwai katon lambu mai shuke-shuke a gaban majalisa da anan ne wasu za su taru su daga kwalaye su ce wani abu da gwamnati ta yi ba dai-dai bane su nuna fushinsu su kuma dage sai an gyara abinda ya ke ba dai dai ba.

Shi ya sa muma a nan majalisa ake sauraron masu zanga-zanga da muzaharori wanda mu muna ganin abinda suke yi yancinsu ne ya ba su dama su yi domin majalisa nan ce wajen kai kuka na abinda ka ga an tauye ma hakki. ‘Yancinka ne, domin ba za su je gidan Shugaban kasa ko Gwamna ba, can za ka ga an hana ka ganinsa, saboda tsaro a wurin, amma mu majalisa sai dai kawai a tsare wani sashi kar masu zanga-zanga su fito su yi ta’adi, su kuma ‘yan majalisa sai su zaga su shigo ta baya domin a ba su yancin da doka ta basu, kuma mu bama ganin su a matsayin masu laifi.

haka kuma daga nan sai a duba ko akwai sako daga Shugaban kasa da ya aiko yana son Majalisa ta sahale masa na ya kashe wasu kudi da za’a yi wa jama’a aiki, ko zai tafi hutu, ko dai wani abu da yake so kamar yadda doka ta tsara.

Duk wannan dai sai an duba kullum, to irin dai wadan nan abubuwa da ake yi a kulli yaumin ya nuna majalisarmu ta takwas ta yi rawar gani na ba da gudunmawa wajen ayyuka da ba da yanci, gami da kokarin warware matsaloli da za su kawo cigaba da bunkasar zaman lafiya a kasa.

Wane irin tasiri wadannan dokoki da kudire-kudure naku suka yi ga jama’a?

To akan wannan matsala ta rashin aiwatar da dokoki da ‘yan majalisar wakilai da ta dattawa da ta jahohi suke yi kuma masu zartarwa ba sa yi, to abinda ‘yan Nijeriya ya kamata su yi shi ne su yi bore, ko su nuna wayewar kansu ta tabbatar da bangaren zartarwa a ko wanne mataki na tarayya ne ko na jiha, wato Gwamna ko shugaban kasa, mutane su tilasta sai an sa hannu kuma an aiwatar da ita in dai Shugaban kasa ko Gwamna ba shi da suka a kanta ita dokar da ya sa hannu tunda dokar kasa ce.

Alal misali a kwanakin baya 14 ga watan Oktoba Shugaban kasa ya sa hannu a kan dokar da za ta samar hukumar raya wannan bangare na Arewa maso Gabas da Boko Haram suka lalata, Shugaban kasan ya sa hannu, amma har yanzu ba a fara aiwatar da ita ba, duk da an tsara komai na nade-naden da za’ayi yadda hukumar za ta kasance ta masu mukamai da inda za su fito duk an tsara, amma har yanzu ba’ayi komai ba.

To wannan jama’a na da yanci na su tilasta wa hukumomin zartarwa da’ayi, domin an ce a bari ya huce shi ke kawo raban wani, kuma aiwatar da doka aikin kasa ne ko ana so ko ba a so dole ne a zartar da ita ba sai wanda ranka yake so ba, kuma ai abin yana da ka’ida na cewa dolene in an sa hannu a kama aiki a tsakanin kwana talatin zuwa mako shida, wannan shi ne abinda doka ta tanada, kuma na yarda da kai ba’a aiwatar da abinda ‘yan Majalisa suka yi na dokoki, wannan ya sa mu ‘yan Majalisa muna cikin bakin ciki na rashin aiwatar da dokoki da ‘yan Majalisa suka yi daga masu alhakin zartarwa a kasar nan.

kuma abun takaici shi ne, tunda aka fara dimokradiyya a kasar duk Majalisun da muke da su akasari sune masu gwamnati kuma su ne masu rinjaye, amma haka na faruwa. kuma an ce in kai wa Shugaban kasa ko Gwamna doka bai gane ba, ko bai amince ba, ya da wo da ita, ita kuma Majalisar Wakilai da ta Dattawa in ta san wannan doka na da muhimmanci ta na iya yi ko da Shugaban kasa bai yarda da ita ba.

Kuna zargin bangaren zartarwa da laifin kin zartar da doka, ku ma fa ana zarginku da kawo wa Shugaban kasa cikas me za ka ce kan wannan zargi?

To idan da wani zargi da aka yi sai ka gaya min in baka amsa, amma in ba sani ba ina so ka sani ko masu biye damu su sani cewa tsakanin Majalisun kasa da masu zartarwa, akwai zargin juna da rashin amincewa da juna, wannan abun haka yake ako ina cikin duniya inda ake mulkin dimukradiyya, domin ni a ganina zaman dole ne ya hada su don haka kullum akwai zargi tsakaninsu, kuma a irin wannan yanayi ne zaka gani cewa, idan majalisa tana kokarin tantance wani abu da ya shafi Shugaban kasa sai ka ji wasu sun shiga kafar yada labarai kamar jarida ko rediyo suna cewa ‘yan Majalisa sun hana Shugaban kasa Muhammadu Buhari aiki ko sun hana Gwamnan jiha aiki haka, kawai sai a ce anki yarda a sa hannu ko ‘yan Majalisa sun ki sahalewa Shugaban kasa ko Gwamna yayi aiki, amma ka lura ko ka bincika jahilcinsu ne, ko kuma an ba su kudi su yi wannan magana ta bata ‘yan majalisa.

Ka yi maganar kowa yana da ‘yanci musamman masu zanga-zanga da masu Muzahara amma duk haka wani lokacin sai ka ga jami’an tsaro suna taho mu gama da masu zanga-zanga Abuja me za ka ce kan wannan?

Eh mana akwai ‘yan caliy boy da sauransu babu shakka na yarda da kai, domin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na amfani da karfi da ya wuce misali, kuma babbar matsalar ita ce, mutane da dama a Nijeriya ba su yarda za su nemi hakkinsu ba.

Amma in ba don haka ba ta yaya za’a ce a yanzu a ce jami’an tsaro na amfani da miyagun makamai akan farar hula akashe wasu a raunata wasu haka kawai kamar kasar dabbobi ba, in da a ce mutane sun san hakinsu da yanzu an daina wannan.

mu a Majalisa da Shugabanmu ne ya je ya ziyarci jami’an tsaro a Legas yayi jawabi cewa, mu a Majalisa hankalinmu yana tashi ganin yadda sojoji suna jihohi kamar 30 wannan abu yana ba mu tsoro a ce sojoji suna kwantar da kura wani a ce Operation yaki da sauransu. Amma soja a ce soja da aka ba shi horo don kare kasa a ce yana arangama da farar hula duk ya ke in abu ya gagari dan sanda za’a iya sa soja, amma ai akwai doka ba ka ci barkatai ba, shi ne ma akwai wata doka ta irin wannan tsarin da ake kira (R.O.I rule of Engagement) wanda ake yi don samar da zaman lafiya, ko doka in abu ya gagari ‘yan sanda ke nan, amma a gaskiya Sojoji da ‘yan sanda na amfani da karfi fiye da kima a Najeriya.

Irin wannan ta sa yanzu haka akwai wasu kungiyoyi na duniya irin su (Amnesty International) da (Human Right Watch) masu karfi ne a duniya kuma sun yi bincike sun tabbatar da aika-aikar Sojojin Nijeriya, kuma kan haka nema yanzu akwai kotun duniya da ke tuhumarsu da laifin keta haddin al’umma a lokutan yaki tana binciken Janar-janar biyar na Sojojin Nijeriya.

Ita wannan kotu ta W.C.T in kuma ta same su da laifi ba shakka sai an fitar da su daga Nijeriya, kuma duk muna da sunansu a Majalisa. Su wadannan Janar-janar su biyar don su fuskanci hukunci akan aika-aika da suka yi akan jama’a farar hula musamman aikin wannan na azabtar da farar hula a lokuta daban daban.

kuma wani abu da nake so a sani na matsalar da wadannan Janar-janar biyar suke ciki shi ne, an hana su biza ta izinin fita daga Nijeriya zuwa kasashen turai da Amurka tun kafin a tuhume su da laifin na ke ta haddin dan adam a kasar haihuwarsu.

kuma ina gaya maka cewa da mu yau Arewa mun san yancinmu kamar ‘yan uwanmu ‘yan kudu da duk wadannan matsaloli ba za su ta’azzara ba kamar Boko Haram da aka yi in a kudu ne ba za ta dau lokaci ba, mutane a kudu za su fito ko a mutu ko ayi rai na kawar da su, ta hanyar matsawa Gwamnati ta dau matakin kawar da su da gaggawa.

Amma a nan Arewa ka ga yadda Boko Haram ta dau lokaci ana kashe mutane ba tare da sarakunanmu da Malamanmu sun dau matakin da ya dace na wayewa irin na mutanan kudu ba, da su ce sai zauna da su an warware matsalar da ko da kuwa ta hanyar sulhu ne, domin su ‘yan Boko Haram ai ‘yan Nijeriya ne, don sun dau makamai ba su ne farkon yin haka ba, an yi ‘yan Biyafara suma makamai suka dauka.

Duk da ba muna goyan bayan ‘yan ta’adda bane, amma dai ina ganin tabarbarewar al’amura akwai laifin ‘yan Bokonmu da sauran masu ruwa da tsaki a Arewa, kuma ina ganin rauninmu da mu kanmu ‘yan Majalisa na kasar nan da kuma duk sauaran masu fada aji a kasar nan irin wannan abu na rauni daga ‘yan Majalisa ya nuna cewa ba wakiltar jama’a mu ke yiba

za mu ci gaba…


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai