Connect with us

WASANNI

Liverpool Ta Ci Karamar Riba Akan Coutinho

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ci ribar zunzurutun kudi har fam miliyan 134 a cinikin Philippe Coutinho da ta sayar wa da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta kasar sipaniya.

Coutinho dan wasan tawagar kasar Brazil, ya koma Liberpool ne da buga wasa daga kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan a shekarar 2013 kan kudi fam miliyan takwas.

Sai dai ranar Asabar Liverpool ta amince da tayin Barcelona a kan Coutinho na fam miliyan 142 kuma tuni kungiyar ta tabbatar da kammala cikin a shafinta na yanar gizo

Tuni dan wasan ya sa hannu kan yarjejeniya a Barcelona ranar Litinin, inda kungiyar ta gabatar da shi a gaban magoya bayanta a ranar Litinin da yamma

Sai dai kuma dan kwallon na yin jinya, inda ake sa ran zai fara buga Barcelona tamaula a watan Fabrairu mai kamawa

Coutinho ya buga wa Liverpool wasannni Firimiya 152, inda ya ci kwallo 41 ya kuma taimaka aka ci 31 a tarihinsa a kungiyar.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai