Connect with us

KASUWANCI

Kungiyar Mahauta Ta Fara Tallafa Wa Matasa 80 Kan Ilimi A Sabon Gari

Published

on


Yanzu haka kungiyar mahauta ta Nijerya,reshen karamar hukumar Sabon gari ta dora dambar tallafa wa matasa tamanin domin ci gaba da karatun sakandare a sassan da suke ciki da wajen jihar Kaduna.

Bayanin wannan tallafi da kungiyar mahauta ta Sabon gari ta  fara bayar wa ga matasa ya fito ne daga bakin babban jami’in watsa labarai na kungiyar , Alhaji Bala Sani, wanda aka fi sani da Bala Bakwai a lokacin day a zanta da wakilinmu da ke Zariya kan wannan aiki da kungiyar ta saw a gaba.

Alhaji Bala Sani ya ci gaba da cewar,daukacin matasa tamanin da suka fara amfana da wannan tallafi,matasa ne da kungiyar ta lura suna yin sana’ar fawa a Kasuwar Sabon gari, karatun da suke yi ya tsaya saboda wasu dalilai ma su yawan gaske,a dalilin haka ne , kungiyar ta bude wannan gidauniyar da nufin ganin matasan sun sami ci gaba da karatun day a tsaya.

Game da yadda za su rika zuwa makaranta su kuma je kasuwa kuwa, Alhaji Bala Bakwai ya ce, kungiyar  ta umurci duk matashin day a ke amfana da wannan tallafi das u rika zuwa kasuwa bayan sun dawo daga makarantar da suke yin karatu.

Domin ganin wannan tsari ya dore kuwa,Alhaji Bala Bakwai ya ce, kungiyar ta kafa kwamiti na musamman da zai sa ido ga karatun matasan, inda aka dora wa ‘yan kwamitin nauyin ziyarar matasan daga lokaci zuwa lokaci,domin tabbatar da ganin matasan na zuwa makarantun da suke karatu ko kuma ba sa zuwa.

Zuwa yanzu babban jami’in watsa labarai na kungiyar ya kara da cewar, akwai tsare-tsare da yawan gaske da kungiyar ta saw a gaba,domin tallafa wa mambobin kungiyar da kuma tallafa ma su a wannan sana’a ta fawa da suke ta ko wane fanni.

Alhaji Bakwai ya nunar da cewar, tun daga lokacin da kungiyar ta kaddamar da wannan tallafi iyayen yaran da suka fara anfana da tallafi suna nuna jin dadinsu da yallafin da ake ba yaransu, ya wannan abu da iyayen suka nuna ma su,ya kara ma su kaimi na ganin sun kara fito da wasu hanyoyi na tallafa wa matasan da suke koyon wannan sana’a ta fawa a babbar kasuwar Sabon garin Zariya.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai