Connect with us

KASUWANCI

Kudin Ajiyar Nijeriya na Kasashen Waje Ya Kai Dala Biliya 40

Published

on


Kamar yadda gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) Mista Godwin Emefiele ya yi hasashe a taron shekara-shekara na kungiyar ma’aikatan banki ta kasa (CIBN) da aka yi Legas a watan Nuwamba 2017 kudin ajiyar kasar nan a kasashen waje ya kai sabon mataki na Dala Bilyan 40 a dai-dai lokacin da bankin ta zuba Dala Miliyan 210  a zagayen farko na kasuwar canji na banki da banki jiya. Kididdigar da aka samu daga CBN ya nuna cewa kudaden ajiyar ya haura Dala Biliyan 40.4 a ranar Jumma’a 5 ga watan 2018 abin da ke nuna karuwar Dala Biliyan 1 tsakanin watan Disamba 2017 zuwa watan Janairu na shekarar 2018.

Da ya ke tabbatar da wadannan alkalummar, mukaddashin darakta mai kula da watsa labarai a CBN Mista Isaac Okarafor ya ce, wannan nasarar ta samu ne sakamako jajircewarsu na tabbatar da kulawa da bukatar kudaden waje a bangarorin tattalin arzikin kasar nan.

Ya bayar da misalin tsarin CBN na hana masu shigo da wasu abubuwa 41 daga kasashen waje daman amfana da garabasar kudaden waje daga kasuwar canji a matsayin babban abin da ya samar da wannan nasarar, “Tsarin ya taimaka wajen rage kudaden waje da ake kashewa wajen shigo da kayayyaki daga kasashen waje daga Dala Biliyan 5 a kowanne wata a shekara 2015 zuwa Dala Biliyan 1.5 a shekarar 2017

Ya ce, CBN za ta hada hannun da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kudade domin tabbatar da kudaden ajiya na kasar nan na ci gaba da karuwa a wannan shekarar.

A rahoton da Jaridar Daily Su ta bayar a makon da ya wuce, ta nuna karuwar kudaden danyan mai a kasuwar duniya ya cilla asusun ajiyar kasan wajen na Nijeriya zuwa dala Biliyan 38.73, an sayar da gangan danyan mai Dala 64.46 a watan Disamba 2017 wani matsayi da aka dade bai kai ba a ‘yan shekarun nan, wannan ne ya karfafa cewa kudin ajiyar zai wuce Dala Biliyan 40 kamar da yadda Shugaban CBN ya yi hasashe. A watan Nuwanba 2017 ya sanar da cillawar kudaden zuwa Dala Biliyan 23 a kididdgar watan Ocktoba 2016 in da ya kuma yi kira ga kanfanoni masu zaman kansu da su taimaka wa gwamnati wajen samar wa da ‘yan kasa aikin yi dokin kawar da talauci.

Emefiele, ya yi wannan karin bayanin ne a yayin da ya ke kaddamar da kanfanin Blue Band Margarine da CBN ta bayar da tallafin YURO Miliyan 10 wajen gina wa a garin Agbara ta jihar Ogun, ya ce wannan nasarar ta samu ne sakamakon matakai na musammam da CBN ta tsayu a kai, wannan ya haifar da karuwar kudaden ajiyar kasashen wajen daga Dala Biliyan 38.2 zuwa Dala Biliyan 40 a halin yanzu, wannan kuma ya sa an samu karuwar dala Biliyan 10 a cikin watanni 7 na 2017.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai