Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Tara Naira Tiriliyan 3 Ta Asusun Bai Daya Na TSA

Published

on


Ministar kudi Kemi Adeosun ta bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta sanar da tara fiye da Naira Triliyan 3 ta tsarin asusun bai daya na TSA, ta yi wannan tsokacin ne a yayin da ta ke gabatar da nasarorin da ma’aikatar ta samu a cikin watanni 24.

Ta ce, gwamnati ta yi tsayin daka ne na ganin ma’aikatu da hukumomin gwamnati na bin tsarin TSA ne saboda alfanunsa wajen kula da kuma tattara kudaden shigan hukumomin ta hanya daya. “Zuwa yanzu gwamnatin tayayya ta hada Naira Tiriliyan 3 a matsayin kudaden shiga tun da aka fara aiwatar da tsarin” in ji ta.

Ta ce, shirin biyan albashi ta tsarin “Integrated Payroll and Personnel Information System (IPPIS)” da na “Information Communications Technology (ICT)” da gwamnati ta bullo da su a watan Afirilu na 2007 ya fara ne da ma’aikatu 7 “Burin wannan tsarin shu ne tattaro da biyan albashi a wuri daya da kuma sanin hakikanin yawan ma’aikata da rage asarar kudade da gwamnati ke yi, muna kokarin sanya hukumomi da dama cikin wannan tsarin nan ba da dade w aba” in ji ta.

Ta kuma yi tsokaci a kan Hukumar Kasa mai kula da zuba jari (NSIA) wadda ke juya Dala Biliyan 1.5 in da ta ce hukumar na da karfin tallafa wa bangaren gine-gine na kasar nan da bashin jarin gudanarwa.

“Sun yi fice ne saboda kyawun tsarinsu domin an shirya su ne ta yadda za su bada cikakkiyar tallafin jarin da zai bunkasa kanfanoni masu zaman kansu na ciki da kasashen waje, tun a shekarar 2014 hukumar NSIA karkashin kulawar Ministan kudi ta shiga wani yarjejeniya tare da kanfanin GuarantCo, wani kanfanin kasa da kasashen Australia da Ingila da Sweden da Swaziland da kuma Netherland ke tallafa wa) domin samar da hanyoyin karfafa hannun jari abin da ya sa aka kirkiro da InfraCredit a farkon shekarar 2017”

“Tsarin InfraCredit na da nufin kawar da matsalolin da ake samu wajen samun bashin kudade a kasuwannin kudade na ciki da wajen kasar nan, kasancewar wannan ne karon farko da aka fara amfani da shirin ba a samu cikakkiyar nasarar da ya kamata ba’.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai