Connect with us

WASANNI

Arsenal Da Liverpool Suna Zawarcin Ivan Rakitic

Published

on


Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa kungiyoyin Arsenal da Liberpool suna zawarcin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Iban Rakiic.

Rakitic, wanda yakoma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona daga kungiyar Sebilla a shekarar 2014 yana ganin kamar komawar dan wasa Coutinho kungiyar zaisa ya daina samun wasanni dayawa yasa yafara tunanin barin kungiyar tun kafin lokaci ya kure masa.

Coutinho yakoma Barcelona ne daga kungiyar kwallon kafa ta Liverpool akan kudi fam miliyan 146 wanda hakan yasa dan wasan yafi kowanne dan wasa tsada a kungiyar tun daga lokacin da aka kafa ta.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Jubentus tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin dan wasan dan asalin kasar Crotia wanda yabuga wasanni 16 a gasar laliga a wannan kakar.

Sai dai kungiyar kwallon kafan ta Barcelona batada niyyar siyar dad an wasan kamar yadda rahotanni suka bayyana sakamakon tana bukatar natasan yan wasa a kungiyar saboda tsufan da yan wasan kungiyar suka farayi wato Iniesta da Sergio Baskuet.

Barcelona tana matsayi na daya akan teburin laliga inda tabawa abokiyar hamayyar ta wato Real Madrid maki 16 bayan buga wasan sati na 18 kuma za ta fafata wasa da kungiyar kwallon kafa ta Celta Bigo a gasar cin kofin Copa Del Rey.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai