Connect with us

WASANNI

Ahmad Musa Zai Bar Leceister City

Published

on


Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Leceister City, Cladio Puel, ya bayyana cewa dan wasan kungiyar, Ahmad Musa, dan wasan tawagar Najeriya ta super Eagles zai iya barin kungiyar a wannan watan na janairu.

Puel, wanda yakoma kungiyar ta Leceister City bayan kungiyar ta kori tsohon mai koyar da yan wasan kungiyar, Craig Shakespare ya bayyana hakane ga manema labarai inda yace kungiyar za ta duba yiwuwar siyar da dan wasan idan hakan ne yafi sauki.

Yace, Ahmad dan wasa ne mai hazaka kuma yanada kokarin ganin yasamu dama a kungiyar sai dai yace kungiyar bata bukatarsa a daidai wannan lokaci.

Yaci gaba da cewa zasu zauna da shugabannin kungiyar domin cimma matsaya akan ko zasu siyar dad an wasan a kasar ingila ko kuma su siyar dashi zuwa wata kungiyar a wata kasar.

Ahmad dai wasa daya yabugawa kungiyar  a wannan kakar a watan Agusta, kuma har yanzu baya buga wasa a kungiyar wanda hakan yasa yake ganin yana bukatar sake sabuwar kungiya domin cigaba da buga wasansa.

Dan wasan mai shekaru 25 a duniya wanda yakoma kungiyar ta Leceister City daga kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow yanason komawa kasar Rasha domin cigaba da buga wasanninsa.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai