Connect with us

SIYASA

Gwamnatin Buhari Ta Janyo Tabarbarewar Tattalin Arzikin Kasa, In Ji Jam’iyyar PDP

Published

on


Jam’iyyar PDP mai adawa ta bayyana cewar gazawar shugaba Muhammadu Buhari, ta hanawa ma’aikatar albarkatun mai samar da mafita ga tsananin karancin mai da har yazu yakici yaki cinyewa a kasar nan har kuma hakan ya janyo tattalin arzikin kasar nan ya samu nakasu.

Jam’iyyar ta kuma yi tir da shirin da Gwamnatin Tarayya ke yunkurin yi na kurdo da tallafin mai.

A wata sanarwa da kakain jam’iyyar na kasa Kola Ologbondiyan, ya sanyawa hannu ya nuna takaicinsa akan yadda shugaba yakin ya sauka daga mukamin ministan mai duk da kiraye-kirayen da ‘yan Nijeriya suka yi masa na ya sauka don bawa wanda yake kwararre da zai kula da

ma’aikatar.

A cewar Jimiyyar, kin daukar shawarar da Buharin ya yi, babu wata mafita ga kasar nan akan matsalar man da yake kara jefa rayuwar alummar kasar nan a cikin halin kuncin rayuwa.

Jam’iyyar ta ce,“ a yanzu kowa ya gane cewar gwamnatin APC ta Buhari burinta shine durkusar da tattalin arzikin kasar nan, maimakon kawo karshen matsalar, sai kara tabarbarar dashi take yi, duk da ikirarin da gwamnatin ta yi a ranar shida ga watan Disambar shekarar 2017 na cewar zata kawo karshen matsalar man a cikin sati daya, amma ta gaza.

Jam’iyyar ta ce, abin da ke kara sanya tsoro bukatar da karamin minister Dakta Ibe Kachikwu ya yi wadda take nuna cewar ana son a cefanar da tattalin arzikin kasar nan ne   don biyan bukatar wasu dake kasashen waje ta hanyar maganar tallafi wanda kwata-kwata ya sabawa ka’idar

kasar nan.

Jam’iyyar ta ce, shi dai ministan wanda ya karyata shirin kara kudin mai kuma yanzu yana kitsa wani sabin shiri yin karin a kai-kaice ta hanyar bawa NNPC damar  ci gaba da sayar da mai akan naira 145 a kan ko wacce lita daya a gidaken manta na mega dake daukacin fadin kasar nan, inda alhalin masu sayar da mai dake zaman kansu su kuma a basu damar sayar da mansu akan yadda sukaga dama a dukkan gidajen mansu.

Jam’iyyar ta kuma zargi  gwamnatin APC a bisa yaudarar ‘yan Nijeriya akan alkawuran data daukar masu na cewar bazata kara kudin mai ba, “duk muna sane da cewar  akwai ‘yan kadan gidanjen mai na NNPC kuma mafi yawancin su basu da man.”

A cewar jam’iyyar ma’anar wannan shine bayan tabarbarar da tsarin gwamnatin APC a yanzu  tana tunanin yadda zata tafiyar da ‘yan kasar nan akan bin ra’ayin masu sayar da mai dake zaman kansu, inda take kokarin yun rufa-rufa akan maganar tallafin mai da biliyoyin naira suke salwanta a kullum a karkashin kulawar su.”

Sanarwar ta kara da cewa, “wannan bukatar zai jefa tattalin arzikin mu a cikin matsala wanda tuni hakan ya fara ragewa kimar yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin ta APC keyi kuma rayuwar ‘yan Nijeriya sai kara shiga cikin wahala take yi.

Jam’iyyar ta ce, naira yanzu batada wata daraja saboda tsare-tsaren da gwamnatin  APC ta zo dasu kuma duk yunkurin kara yin wani sabon tsari, zai kara takurawa jama’a ne da kara jefa kasar a cikin halin ni ‘yasu.

Jam’iyyar ta yi nuni da cewa, ‘yan kasar nan a yanzu suna sane da cewar gwamnatin tana ikirarin tana yaki da cin hanci da rashawa amma sai gashi an sameta dumu-dumu akan yin amfani da maganar badakalar cire tallafi kuma  APC ta nuna goyon bayanta na matakin  da gwamnatin tarayya ta dauka rage kudin mai.

Jam’iyyar ta ce, sakataren yada labaran  APC na kasa Malam Bolaji Abdullahi a hirar sa da jaridar Guardian yace an dauki  matakin ne don tallafawa ‘yan kasar nan don kare su daga yin wani sabin tsari na man.

Abdullahi ya ce, tallafin cire tallafin da gwamnatin  Buhari ta yi, zai tabbatar kare

almundahana.

Yace, APC ta nuna ja akan sahwarar rage  rage kudin man, abin shine wannan zabin  da ya kamata gwamnati ta dauka kuma koda wannan zabin ya zo ne da tsadar sa ko kuma tattalin arziki ko sanya harkar siyasa a cikinsa.

A karshe gwamnati zata dauki matakin da ya dace don amfanin ‘yan kasa.

Maganar tallafi kuwa, ya samu asali ne daga gwamnatin data gabata saboda cin hanci da rashawa da ya dabai baye tallafin.

Idan kana bibiyar tattaunawar a tsakanin watan Janairun shekarar 2012 akan maganar cire tallafin, zakaga cewar, ‘yan Nijeriya sun soki hakan a wancan lokacin.

Sun yi sukar domin wasu ‘yan tsiraru sune kawai suke samun kudi akan harkar fiye da kasar.

A saboda yadda aka yin amfani da alundaha wajen kaddara da tallafin hakan ya sanya ‘yan kasar nan suka soki tallafin shi kanshi.

A saboda haka, matakin rike tallafin munyi imanin ra’ayi na kowa wane dan Nijeriya kuma anyi shine don a tabbatar da an cire masu dukkan wani nauyi.

A wata sabuwar kuwa, shugabar mai tsawatarwa ta marasa rinjaye ta majalisar dattawa   Biodun Olujimi, ta zargi shugabancin kasar akan gazawar data jefa alummar kasar a cikin halin kuncin rayuwa.

A cewarta, gwamnatin APC bata da wani cikakken tsari a kasa akan yadda zata tafiyar da shugabacin kasar nan a lokacin data karbi ragamar mulki a shekarar 2015.

Olujimi ta furta hakan ne a satin da ya gabata lokacin data karbi bakuncin alummar mazabarta dake Ekiti ta Kudu a taron walimar data shirya a gidanta dake Omuo a cikin jihar Ekiti.

Tsohuwar mataimakiyar gwamnan ta ce,” PDP ta mika kasar nan a hannu gwamnatin APC a shekarar  2015 lokacin kasar tanada kyau, amma a yanzu mutanen kasar nan sun ga ban-banci a yau.”

A cewarta,” a shekaru sha takwas na karshe mulkin dimokiradiyya, ban ban taba ganin gwamnati da aka kasa gudanar da ita sai a wannan gwamnatin  ta APC maici, kuma sun karbi mulki ne kawai, akan akida, amma a zahiri, basu da wani kyakyawan tsari don shugabantar kasar, kuma basu san abin da zasu yi ba.”

Taci gaba da cewa, “ muna dai tara kowa da kowa kuma kowa yanayin abin da yaga dama ne, kuma an jefa mutane a cikin kngin talauci.”

Ta bayyana cewar, sunce mu bazamu iya ba, amma ban san abin da su suke nufi ba, domin yanzu an jefa mutane cikin kangin talauci.

Ta ce, “ a halin yanzu babu wasu guraban aiki a ko ina a kasar kuma farashin kayan masarufi sai kara tashin gwaron Zabo suke yi kuma hanyoyi duk sun lalace babu wutar lantarki talakawa kuma basa iya ciyar da kansu basu kuma iya biyan kudin makarantar ‘yayansu wasu kuma duk an mayar dasu mabaratan karfi da yaji.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai