Connect with us

SIYASA

Dalilin Da Ya Sa Bana Gudun Jama’ar Da Suka Zabe Ni –Hon. Mai Fada

Published

on


HONARABUL MAI FADA BELLO KIBIYA shi ne dan Majalisar Jiha mai wakiltar karamar hukumar Kibiya, Dan majalisar da tarihi ya tabbatar da shi a matsayin dan Majalisar daya tilo da ba ya gudun jama’arsa, su ma kuma haka jama’ar Kibiya basa gudunsa, guda cikin ‘yan gaba dai gaba dai ta fuskar jadadda yakin ganin Gwamna Ganduje ya ci gaba da kwararawa Kanawa ayyukan alhairi. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, dan majalisar ya bayyana irin fatan da suke yiwa makomar Jihar Kano nan ba da jimawa ba, haka kuma ya yi gudu har da zamiya wajen bayyana wasu daga cikin nasarorin da suka cimma kasancewar sa a majalisar jihar Kano. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance;

Za Mu so jin wanda muke tare dashi a halin yanzu?

Alhamdulillahi kamar yadda aka sani ni sunan Honarabul Mai Fada Bello Kibiya dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Kibiya a majalisar dokokin Jihar Kano karkashin Jam’iyyar APC.

Honarabul Mai Fada kamar yadda aka sani kuma ake gani yanzu haka ana iya cewa aski fara zuwa gaban goshi, musamman ganin kakar zaben shekara ta 2019 ta fara gabatowa, shin ko me zaka ce dangane da batun alkawurran da aka yiwa al’umma alokacin yakin neman zabe?

Gaskiya ne ko shakka babu an fara jin motsin gabatowar lokacin zabe mai zuwa, amma fatan da muke yi ga jama’a shi ne akwai bukatar kara baiwa Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje damar nutsuwa domin samun sukunin ci gaba da ayyukan alhairi da aka sa gaba. Kuma ina tabbatarwa da Kanawa yanzu ido ba mudu ya san kima, wanda duk ke kishin ci gaban Kano da Kanawa dole ya jinjinawa Khadimul Islam idan akayi la’akari da wasu muhimman abubuwa da suka banbanta shi da sauran Gwamnonin Najeriya.

Da farko dai bari na fara da yiwa jama’a gwari gwari domin batun albashi na cikin abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma na yau da kullum, ba wai ga mai daukar albashin ba kadai, a’a ko ‘yan kasuwa na fahimtar halin da ake ciki matukar aka samu albashi ko akasin haka, wannan kuma a Jihar Kano Allah ya tarfawa garinmu nono, domin tun zuwan wannan Gwamnati mai albarka ba’a taba yin batan watan biyan albashi ko fansho ba.  Saboda haka wannan abin a yaba ne a kuma a jinjiniwa wannan gwmanati.

Shi batun albashi shi ne kadai ma’aunin da ake iya dora nasarar gwamnati a kansa?

‘yan Jarida kenan ana baku kuna ga hannuna ai jawabin nake maka dalla dalla, batun albashi cikin ayyukan wannan Gwamnati ai lafila ce, domin ai ku ‘yan jaridu shaida ne  irin tulin basukan da Gwamnatin Ganduje ta Gada, sannan kuma da halin masassarar tattalin arziki da aka fuskanta a kasa baki daya, kai ka sani ko hasidin iza hasada ya san Ganduje ya ciri tuta. Saboda haka ne ma kake ji ana ta yiwa masa luguden lambobin yabo da kuma sambarka.

Kana cikin wakilan da karamar hukumar ka ta Kibiya ta amince da ka wakilce su domin kawo mata ayyukan ci gaba, shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu  zuwa yanzu?

Ban so a ce ni zan amsa wannan tambaya ba domin gudun kar na zama magori wasa kanka da kanka, kamata ya yi a ce  al’ummar Kibiya ka yiwa wannan tambaya. Amma duk da haka alhamdulillahi kulluma ina kara yiwa Allah godiya domin muna yin bakin kokari domin ganin mun samar da ayyukan more rayuwa da kuma ci gaba al’ummar da suka sahalle mana wakiltarsa a majalisar dokokin Jihar Kano. Aikin dan Majalisa shi ne gabatar da dokoki da kudurce kudurcen da zasu kare muradin al’umma, sannan kuma aikinmu ne san na mujiya domin ganin duk dokar da muka samar an tabbatar da yin aiki da ita.

A nan dole mu godewa mai girma Gwamna Gandujen domin yana bamu dukkan goyon bayan da majalisa ke bukata wajen gudanar da ayyukan majalisar ba tare da yin Katsalandan ba.

Honarabul ko gaskiya ne da ake cewa Gwamna duk ya sanya ku cikin aljihunsa?

Ina tabbatar maka  idan ma akwai inda ya wuce aljihu can ya sanya mu, domin dukkan mu da Gwamna Al’ummar Jihar Kano ce a gabanmu, ciwo daya ke damun mu shi ne yadda za’a samarwa da Jihar Kano ci gaba mai dorewa. Idan kuwa haka ne muna yiwa Allah godiya da ya hada kanmu wajen yiwa Kano da Kanawa abinda suka tura mu dominsa. Kuma waccan magana ai rashin sanin ya kamata ne a ce wai gwamna ya sa ‘yan majalisu a aljihu, ashe ma ba jam’iyya daya muke ba da har sai anyi wani abu na rashin sanin ya kamata. Idan ba manta ba duk fadin kasarnan Jihar Kano ce Jiha Daya tilo da Jam’iyya APC ta lashe zabe ko kujera daya wata Jam’iyyar adawa bata samu ba. Wadanda Allah ya yiwa haka kuma mai rage a gabansu idan ba cika alkawurran da aka yiwa jama’a ba alokacin yakin neman zabe.

Za mu so ka dan tsakurawa Mai karatu kadan daga cikin abubuwan da aka samarwa al’ummar Kibiya?

Alhamdulillahi akwai abubuwa da yawa wanda kila irin wannan dan lokacin ba zai bada damar bayyana su baki daya ba, amma dai kamar yadda aka sani akwai batun harkokin lafiya wanda mun yi bakin kokari wajen samar da wuraren sha maganunuwa, samar da hanyoyi a mazabu  daban daban a karamar hukumar Kibiya, sai kuma samawa mata da mata sana’u tare da samar masu dan jarin da zasu ci gaba da jalautawa. Harkokin ilimi na cikin abubuwan da gwamnatin nan tafi mayar da hankali, wannan tasa majalisa muka amince da fara ciyar da daliban makarantun firamare har kwai ake bayar a lokuta daban daban.

Kwanakin baya an ji ka kaddamar da wani shirin bayar da tallafi ga jami’an tsaro a karamar hukumar Kibiya, shin ya ya al’amarin yake?

Gaskiya na yi wannan turani domin tallafawa jami’an tsaro wanda kullum suke aiki ba dare ba rana wajen tsare rayuka da dukiyar al’umma. Wanann ya sa bayan dogon tunani na yi la’akari da haka tare da raba motaci kirar Sharon har guda hudu, Ya zama wajibi a matsayinmu na wakilan al’umma sauke nauyin da ya kamata mu sauke na alkawarin  da muka dauka na yin duk mai yiwu wajen taimakawa duk wani bangare da zai kawo ci gaban al’umma.

Kuma alhamdulillahi ina matukar farin ciki da irin goyon bayan da jama’ar Kibiya suke baiwa wakilcin da suka tura mu, haka kuma ina kara godiya ga iyayen kasa musamman Hakimai, dagatai da masu unguwanni, saboda haka  ina tabbatarwa da jama’ar Kibiya cewa da yardar Allah dan su Mai Fada Bello ba zai basu kunya ba.

Wannan tasa muka raba motoci hudu kirar Sharon kantara kanatara ga Jami’an rundunar ‘yan sandan Karamar hukumar Kibiya da Rundunar Hisbar Karamar hukumar Kibiya, jami’an Kashe gobara da kuma ‘yan kungiyar tsaro ta sa kai ( Cibil Defence), wadannan kungiyoyi kowanne ya yi hafzi da wannan mota ta ke a wurin da aka gudanar da shirin.

Kana cikin ‘yan majalisar da aka tabbatar da baka gudun jama’ar da suka zabe ka, shin ko mene ne sirrin hakan?

Alhamdulillahi a tsari na ko irin tunanina banga dalilin gudun jama’ar dasu ka nuna kaunar ganin ka wakilce su a wasu matakai daban daban ba, kuma ita gaskiya daya ce ni abinda na gamsu shi ne duk abinda aka nema idan kana da iko ka yi shi alokacin da aka bukata, idan ba ka da iko kayi bayani mai dadi tare da kwantar da hankalin masu wannan bukata. Kila a ganina wannan ce tasa jama’a basa guduna kamar yadda nima bana gudunsu.

Wannan tarbiyya ce wadda gadonta muka yi tun daga gida, saboda haka muna tabbatarwa da jama’ar Kibiya  insha Allah ayyukan ci gaban al’umma yanzu aka fara.

An fara kiraye-kiraye kan bukata sai ka sake fitowa wannan takara a kakar zabe mai zuwa, shin ko me zaka ce kan haka?

To shi al’amarin ai na Allah ne kuma shi ke bada mulkin nan ga wanda ya so alokacin da yaso, na tabbata cewa jama’a gamsuwa da wakilcin da muke ya sa suke kwadayin ganin mun sake ci gaba da rike wannan matsayi, saboda haka ina kara baiwa Jama’a hakuri domin akwai sauran lokaci, babban abinda muke roko ita ce addu’a domin samun damar ci gaba da ayyukan alhairi cikin saura lokacin da  muke dashi. Ina tabbatarwa da al’ummar Kibiya cewa insha Allahu dansu ba zai basu kunya ba, domin bani da wani abu da ya wuce kaunar hidimtawa jama’ar karamar hukumar Kibiya a kowane mataki suke bukata.

Mene ne sakonka ga al’ummar Kibiya wadanda suka sahalle maka wannan wakilci?

Da farko ina godiya kwarai da gaske bisa kauna, yakana, zumunci da soyayya da ake nunawa Mai fada Bello, sannan kuma ina kara mika irin wannan godiya ga iyayen kasa musamman hakimn Kibiya, dagatai da masu unguwanni, sai kuma malamai wadanda kullum suke addau’a ba dare ba rana wajen samun nasarar wannan gwamnati. Muna fatan Jama’a za’a ci gaba da kyautatawa Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin samun damar kammala ayyukan da aka sa gaba. A karshe ina kara kira da babbar murya da cewa kowa ya tabbatar da cewa ana lura da harkokin lafiya da kuma duk wani al’amari da zai inganta lafiyar mu data iyalanmu.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai