Connect with us

KASUWANCI

Bankunan Nijeriya Sun Dakatar Da Ciran Kudi Daga ATM Ga Wadanda Ke Kasashen Waje

Published

on


Binciken da wakilinmu ya gudanar, ya tabbatar da cewa wasu Bankunan Kasarnan, sun dakatar da baiwa masu hulda da su izinin ciratar kudadan waje da suka hada da, Dalar Amurka, Yuro da Kuma Fam na kasar Ingila, a duk lokacin da suka fita kasashen na waje.

Wannan matakin dai da Bankunan suka dauka ana jin tsoron zai saka ‘yan kasuwa da kuma masu fita yawon shakatawa a cikin mawuyacin hali.

Su ma daliban da ke yin karatunsu a kasashen na waje, wadanda kuma yawancinsu sun dogara ne a kan ciran kudaden hidiman karatun su da sauran hidindimun su ta hanyar mashinan ciran kudin na ATM ne, su ma za su iya fuskantar matsala.

Binciken da wakilin na mu ya yi, ya gano cewa Bankunan sun dauki wannan matakin ne a bisa yawan faduwar darajan kudin mu na Naira, wanda hakan ya janyo wa Bankuna da yawa asara mai yawa a sama da tsawon shekara guda, da kuma asarar da suke hangen za su ci gaba da tafkawa a nan gaba sabili da faduwa da kuma rashin daidaiton darajar kudin namu na Naira. A cewar Bankunan hakan ne ya tilasta masu dakatar da baiwa abokanin cinikayyan na su izinin ciratan kudin wajen daga mashinan na ATM.

Duk da hakan, wasu Bankunan da suke samun riba daga irin wannan cinikin, da kuma wadanda suke da takwarorin su a kasashen na waje da suke saukaka masu cinikayyan na su, su kam wannan matsalar ba ta shafe su ba, don haka suna ci gaba da gudanar da harkokin na su ta mashinan ATM a kasashen na waje.

Wani babban ma’aikacin Banki da bai so mu bayyana sunansa ba, ya shaidawa wakilinmu cewa, “Kowane Banki yana da na shi dalilin na kin bayar da izinin cire kudin ta ATM, a waje. Wasu Bankunan sun tafka asara ce mai yawa a shekarar da ta gabata, lokacin da darajar Naira ya fadi kasa warwas, shi ya sanya a yanzun suke kokarin takaita hadarin da suke hange a kan hakan.

“Iren wadannan Bankunan, ba su da wani shiri na sake farfado da wannan tsarin. Wasu kuma a halin yanzun suna kan bincikar hanyar dakile wadanda suka mayar da wannan hanyar a matsayin kasuwanci ne tukuna kafin su ci gaba da bayar da izinin. Da dai sauran dalilai da dama da suka hana wasu Bankunan dakatar da wannan hanyar.”

Binciken mu, ya tabbatar mana da cewa, kusan mafi yawancin Bankunan sun ci gaba da baiwa abokanan huldar su daman yin cinikayya ta wadannan hanyoyi a kasashen wajen, amma kuma akwai da yawa daga cikin Bankunan da suka dakatar da wannan tsarin na yin cnikayya ta hanyar amfani da mashinan na ATM, a kasashen wajen, ba kuma tare da sun ce ga lokacin da za su dawo da hakan ba.

Daga cikin Bankunan da binciken namu ya nu na mana cewar sun dakatar da hakan sun hada da, Bankunan, ‘Guaranty Trust Bank Plc, Fidelity Bank Plc, Stanbic IBTC Bank da kuma, Standard Chartered Bank.’

A lokacin da wakilinmu ya kirayi teburin sauraron koken Jama’a ta waya na Bankunan, sun tabbatar masa da cewa, lallai sun dakatar da wadannan tsare-tsaren na su, ba su kuma bayyana masa dalili ba, ko kuma zuwa yaushe ne za su ci gaba.

Wasu daga cikin mutanan da kan yi amfani da wadannan hanyoyin sun bayyanawa wakilinmu cewa, tabbas Bankunan Nijeriya suna kashe kudade masu yawa a sakamakon masu amfani da wadannan hanyoyin cinikayyan a kasashen na waje.

Suka kuma ce, tsoron masu yin amfani da wadannan hanyoyin wajen fitar da kudaden ta hanyar da ba ta dace ba,yana daya daga cikin ginshikan dalilan da suka sanya tilas Bankunan su dakatar da dibar kudin ta wadannan hanyoyin.

Suka kuma kara da cewa, wasu kuma Bankunan sakamakon karancin Dala da aka samu a shekarar da ta shige ne, ya sanya su tilas yin takatsatsan wajen amfani da ajiyarsu ta kudaden wajen.

Sakamakon kuma faduwar darajar danyan Man Fetur a kasuwannin duniya, hakan ya sanya aka sami karancin Dala wanda kuma shine ya kara tabarbara tattalin arzikinmu, wanda har ila yau kuma shine ya shafi ayyukan wasu Bankunan, har ya sanya su tilas su hana barin ana ciratar kudin ta hanayar amfani da mashinan na ATM, a kasashen na waje, da duk sauran hanyoyin da ake amfani da su ta yanar gizo.

Sai dai kuma, a lokacin da aka dan sami saukin cinikin kudaden na waje ta hanyar ‘Fored’ a wannan shekarar, wasu Bankunan sun sanar da dawowa da wadannan hanyoyin da a da suka haramta.

Wasu daga Bankunan da suka dawo da wannan hanyar ka’in-da-na’in sun hada da, ‘United Bank for Africa Plc and First Bank of Nigeria Limited. Similarly, Zenith Bank Plc, Ecobank Nigeria and Skye Bank Plc’duk sun sanar da cewa, masu hulda da su, a yanzun suna iya ci gaba da yin amfani da wadannan hanyoyin.

Sauran kuma dai har yanzun suna cewa ne, kasuwar ba ta ba su damar yin hakan ba tukunna.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai