Connect with us

LABARAI

Badakalar Dawo Da Maina: Kotu Ta Kware Wa Ministan Shari’a Baya

Published

on


Mai shari’a Binta Murtala-Nyako ta babbar kotun Abuja ta ki amincewa da bukatar Ministan Shari’a na Kasa Abubakar Malami (SAN) na kotu ta dakatar da majalisar kasa daga bincikar badakalar dawo da tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa a kan gyare-gyaren fansho Abdulrasheed Maina bakin aiki kwananakin baya. An dagatar da Maina daga bakin aiki ne a bisa zargin almundahana a kwamitin gyare-gyaren harkan fansho da ya shugabanta. A na kuma zargin Malami na daga cikin jami’an gwamnati da suka bayar da izinin mayar da Maina bakin aiki, abin da ya jawo ceckuce a fadin kasa Nijeriya.

A ranar 24 ga watan Oktoba ne Majalisar Dattijai ta umurci kwamintinta da ke kula da harkokin ma’aikata da cikin gida da shari’a da su binciki hanyoyin da a ka bi har aka dawo da Maina bakin aiki, ita kuwa Majalisar wakilai tunu ta shiga bincike domin  gano wadanda ke da hannu a dawo daMaina bakin aiki.

A lokacin da ya gurfana a gaban kwamitin majalisar wakilai,Malami ya musanta hannu a badakalar da ta kai ga dawo da Maina.

Da aka gabatar da shari’ar, Mai Shari’a Nyako ta ki amincewa da bukatar da bangaren Malami suka bayar in da ta umurci daya bangaren domin su gabatar da dalilansu na abin da ya sa ba za a amince da bukatar da ake nema ba. Daga nan ne kotu ta daga zaman zuwa ranar 15 ga watan Janairu domin ci gaba da saurarron karar

A cikin karar dai Ministan Shari’a na bukata wa kotu ya na son ne ta yanke hukunci a kan ko majalisar kasa na da hurumin bincikar matsalolin da suka shafi daukan aiki da zuwa aiki da sallama aiki da dawo da ma’aikaci bakin aiki da kuma kara wa ma’aikaci girma.

Ya na kuma bukatar kotu ta zartar da cewa abubuwan da suka shafi zuwa bakin aiki da sallama aiki da dawo wa bakin aiki da kuma karin girma ba sa cikin ababen da majalisa za ta iya bincika kamar dai yadda ya ke a tsarin dokokin kasar nan na shekarar 1999 da ka yiwa kwaskwarima.

Malami na bukatar kotun ta zartar da cewa, Majalisar kasa ba ta da hurumin sa hannun a alamuran da suka shafi daukar aiki da zuwa wurin aiki da sallama aiki da dawo wa bakin aiki da kuma karin girma, wadannan wasu al’amura ne da suke karkashin kulawar Hukumar Daukar Ma’aikara ta kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya hakasta mata. Ya na kuma kara neman kotun ta zartar da cewa doka bai ba majalisar ikon bincikar yadda a ke dauka aiki da zuwa wurin aiki sallama aiki da dawo wa bakin aiki da kuma karin girma, wadannan wasu al’amura ne da suke karkashin kulawar Hukumar Daukar Ma’aikara ta kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Ministan shariar ya gabatar da hujjar cewa ikon bincike da sashi na 88 (1) na tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa dokoki yana da iyaka saboda haka dole su gudanar da duk binciken da za su yi a karkashin sashin 88 (1) na kundin tsarin mulkin kasa na shekara 1999

Ya kuma bayyana cewa a matsayinsa na babban mai kula da dokoki na kasa, ya na da hakkin ganin dukkan hukumomi da bangarorin gwamnati suna bin tanade-tanaden dokoin kasar nan.

Daga nan ya karkare da cewa, ba zai kyautu Majalisar dokoki ta mayar da kan ta wata hukumar bincike ba, ya kuma nemi kotu ta yi la’akari da hukuncin da wata kotu ta yanke a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/65/2013.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai