Connect with us

BIDIYO

SHARHIN FINAFINAI: Sharhin Fim Din ‘Ciki Da Raino’

Published

on


Tare Da: Saddika Habib Abba 09097438402 habibsaddik[email protected]

Suna: Ciki Da Raino

Tsara labari: Nazir Adam Salihi

Furodusa: Ibrahim Sinana

Bada umarni: Falalu Dorayi

Kamfani: TJ Multipurpose Concept

Jarumai: Adam A Zango, Sulaiman Daushe, Falalu A. Dorayi, Hadiza Aliyu Gabon, Ibrahim Sinana, Umma Shehu, Tijjani Asase, Hauwa Malali

 

A farkon fim din an nuna Shamaki (Sulaiman Bosho) ya na zaune a wurin sana’arsa ta gadi, matarsa Zara’u (Hadiza Gabon) ta bugo ma sa waya ta shaida ma sa cewar a asibiti an tabbatar ma ta da cewar ta na da juna biyu. Shamaki ya nuna murnarsa da jin dadinsa sosai sakamakon wannan albishir da a ka yi ma sa a lokacin har ya zo ya rabawa abokan aikinsa kudi.

A wani bangaren kuma na fim din an nuna Alhaji Bashir (Ibrahim Sinana) tare da matarsa Sa’ade (Hauwa Malali) ita ma ta nuna ma sa cewar ba ta da lafiya kuma da alamun ta na da juna biyu. Shi ma ya nuna jin dadinsa sosai, sannan ya umarce ta da su je asibiti domin likita ya tabbatar mu su.

A bangaren gidan Nafi’u (Falalu A. Dorayi) shi kuwa wata budurwarsa, Fadila (Umma Shehu), ya yiwa ciki ta zo gidansa ta tare ta tabbatar ma sa da cewar sai ta haife abinda ya ke cikinta, sannan ta tafi kauye ta direwa mahaifinsa. Nafi’u da Fadila su ka buga su ka buga a kan cewar shi ba za ta zauna a gidansa ba, sannan shi cikin ma bai yarda nasa ba ne, amma daga karshe Fadila ta tubure har sai hakura Nafi’u ya yi, domin a yadda a ka nuna Fadila ta fi shi sanin kan tsiya.

An nuna Alhaji Bashir ya kawo matarsa asibiti, domin a tabbatar ma sa da cikin matarsa. A lokacin su ka hadu da Shamaki shi ma ya kawo matarsa. Kwatsam shi ma Nafi’u sai ga shi ya kawo Fadila, domin a tabbatar ma sa, saboda da ma shi tun farko ya karyata cewar akwai cikin.

Kowaccensu Dakta (Adam A Zango) ya ba ta gwaji, a ka je aka tabbatar da cikin sannan a ka ba su lokacin da za su dinga zuwa awo. A wannan zuwan da su ke yi su na kawo matan awo a nan a ka saba da Bashir da Shamaki da kuma Nafi’u, amma duk wannan abinda a ke yi su a zatonsu Nafi’u da Fadila mata da miji ne, domin idan za su yi masifarsu gefe su ke komawa su yi.

Wadannan cikkunna na matan kowanne ya janyo ma sa wahala; kowacce ta dinga wahalar da mijinta; yau wata ta ce goruba za ta ci, wata ta ce fasadabur, wata ta ce goba. Kuma idan sun sha wahala sun nemo sun kawo mu su, sai su ce ya fita daga ransu. Haka kowacce ta cigaba da wannan diramar har lokacin da kowaccensu ta haihu. Sai kuma su ka maida raino hannun mazan. Ita Fadila budurwar Nafi’u ta haifi namiji, ita kuma Zara’u matar Shamaki ta haifi mace, ita kuma Sa’ade matar Alhaji Bashir ta haifi namiji.

Haka zumunci ya kullu tsakaninsu tamkar da ma can sun san juna. An nuna hatta rainon a guri daya su ke yi mu su. Idan banda wahalar da su da matan ke yi babu abinda su ke yi. Su ne su ke yi mu su rainon yaran, goyo, rarrashi duka har sai lokacin da wani dan duniyar abokin Nafi’u Namaroko (Tijjani Asase) ya zo daga Legas ya koya mu su dabarun yadda za su dinga yiwa matan nasu su daina wahalar da kansu.

A cikin abinda ya koya mu su ya nuna mu su cewar idan yaran su na kuka, to su dinga kyale su, idan su ka ga haka da kansu za su dinga kulawa da ‘ya’yannasu, domin uwa ta fi kowa son danta; uba ya na iya damka dansa a hannun hukuma, idan ya yi laifi, amma duk runtsi uwa ba ta iyawa. Haka kuwa a ka yi yaran su na fara kuka su ka yi burus su ka kyale su, sai ga shi kowaccensu ta dauki danta ta na jijjigawa. Alhaji Bashir da Shamaki da Nafi’u su ka nuna jin dadinsu sosai da abinda Namaroko ya yi mu su, domin da ma sun gaji.

A lokacin Nafi’u yaja abokinsa Namaroko gefe a kan ya ba shi shawarar ya ya zai yi ya rabu da nasa jaririn da Fadila uwar jaririn tunda an same shi ne ba ta hanyar aure ba? Namaroko ya ba shi shawarar kawai ya zo ya bi shi su gudu Legas su cigaba da shan sha’aninsu a can. Namaroko ya shaida ma sa cewar, shi zai wuce Kaduna a ranar. Ya fada mi shi cewar ya biyo shi Kadunan washegari, daga nan sai su wuce Legas. Nafi’u ya yarda da shawarar Namaroko ya hada kayansa, washegari ta na yi Fadila ta na bacci ya saka kaya a mota ya dauki hanyar Kaduna. Sai da ya yi nisa sai ya ji kukan jariri a bayan motarsa. Ya na dubawa sai ya ga ashe bai sani ba Fadila ta saka masa dansa a bayan motarsa. Takaici ya saka Nafi’u ya rushe da kuka, don babu tafiya tunda abinda a ke gujewa ga shi a bayan mota.

 

Abubuwa Birgewa:

1- An nuna tsantsar kulawa tsakanin miji da mata, musamman a lokacin da mace ta ke da juna biyu

2- Jaruman sun yi kokari wurin isar da sakon

3- An yi amfani da kayan aiki masu kyau, musamman kyamara da kuma abin daukar sauti

 

Kurakurai:

1- Akwai wurin da Zara’u ta ke bugowa Shamaki waya ta ke shaida ma sa ta je asibiti an shaida ma ta ta na da ciki kuma daga bisani sai mai kallo ya ga sun kuma zuwa asibiti a tabbatar mu su. Shin sun manta Zara’u ta je asibiti ne kuma a can a ka tabbatar ma ta ta na da juna-biyun?

2- Akwai wurin da su Fadila su ke zuwa sayen kayan marmari da Nafi’u ta ke fadawa mai kayan marmarin ita koriyar tufa ta ke so, ya ce ‘to’, kuma sai mu ka ga ya dauko jar tufa ya saka ma ta alhali sharadin da ta saka bai cika ba kuma bai ce babu ba. kuma da ya kawo ta bude ta fara ci ba a ga mamaki a fuskarta ko ta nun aba haka ta ce ma sa ba.

3- An nuna cewar fim din ya na magana ne a kan Musulmai kuma Hausawa da al’adarsu, amma sai mu ka ga Fadila ta tare a gidan Nafi’u na tsawon lokaci har ma ta haife juna-biyun jikinta ba tare da hakan ya janyo abin magana a unguwa ba. A zahirin addini da al’adar Bahaushe hakan ba ya faruwa, domin ba muharraman juna ba ne, babu hurumin da ya ba ta damar zama a gidansa. Idan ma za a yi hakan sai dai a ce daga baya ya aure ta tunda cikinsa ne ta haihu a gidansa, amma ba wai su cigaba da irin wannan zama wanda addini da al’ada su ka haramta ba kuma ba tare da komai ya biyo baya a cikin al’ummarsu ba.

4- Kwatsam! Bayan matan uku sun haihu sai mu ka ga mazajensu da yara a wani lambu su na raino. An gaya ma na cewar sun kawo matansu asibiti, amma sai mu ka ga matan nasu a zaune cikin lambu su na shakatawa da lafiyyen abinci. Ya dace a ce an nuno su a cikin asibiti kuma a fadi dalilin da ya kawo su, ba wai a nuno ma na su a lambu ba, domin duk mai kallon da ya ga wajen ya san ba asibiti ba ne.

5- Shin fim din a birni a ka dauke shi ko kuma a kauye? An rikitar da masu kallo domin wani wurin sai a gan shi birni, amma wani wurin kuma a kauye musamman hanyoyin.

 

Karkarewa:

Fim din ya kayatar, amma babu sakonni masu karfi a ciki kuma wasu abubuwan ba a nuna karshensu ba.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai