Connect with us

KASUWANCI

Ginin Bangaren Filin Jirgin Sama Na Abuja Zai Ci Karin Dala Miliyan 400

Published

on


Karamin Ministan Harkokin Jiragen Sama Hadi Sirika ya ce, sabon bangaren filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja za ci Karin Dala Miliyan 500 kafin a kammala.

Sirika ya yi wannan bayanin a yayin da ya ke zagaya wa in da ake gudanar da aikin, in da ya nuna takaicin sa a bisa rashin cika alkawari da gwamnatin tarayya ta yi na kammala aikin a watan Disamban shekarar da ta gabata, ya ce hakan ya faru ne sakamakon karin aikin da aka yi a kan abin da aka tsara tun da farko domin samun cikakken amfanin da ake fata.

“Abin takaicin ne wasu bangaren aiyukan na da wahalar gaske hakan zai haifa da jinkiri, babban matsalar ma ita kokarin hada tsohuwar hanyar saukan Jirgin da sabuwar ginin”

Ya bayyana cewa, ana gudanar da aikin ne da taimakon bashin Dala Miliyan 500 daga kasar Chaina, Nijeriya za ta ba da nata kason na gudanar da aikin na Dala Miliyan 100 abin da ya kama Dala Miliyan 600 ke nan domin kammala aikin ana bukatar karin Dala Miliyan 400” Inji shi.

Sirika ya kara da cewa, gwamnati za ta yi nazarin yadda za ta anfana da filin girgin saman duk da matsalolin da a ke fuskanta, ya kuma lura da cewa ana bukatar dimbin kudade domin samar da ruwa da wutan lantarki da matsar da dakin sarrafa tafiye-tafiyen jirage da samar da ma’aikatan kashe gobara da kuma hanyar da ta hada Sabuwa da tsohuwar bangaren filin saukan Jiragen.

Ya kara da cewa, matsalar da aka samu ya faro ne tun lokacin da aka bayar da kwangilar, da aka fara aiki sai aka lura da karuwa da giman aiyukan. Da farko kuma an dauka aiki ne dan kadan. Ya kuma ce taswirar filin jirgin saman na asali ya samar da hanyoyin fadada shi in bukatar haka ya taso, musamman idan ana samun karuwar fasinjoji.

Ministan ya ce, dan kwangilar da ke gudanar da aiyukan ya tabbatar masa cewa, nan da watan Maris na wannan shekarar wani bangaren na filin Jirgin saman zai fara aiki gadan-gadan, Wakikin kanfanin “China Cibil Engineering Construction Company” da ke gudanar da aiyukan ya ce, a halin yanzu aikin ya kai kashi 87 kuma da yardan Allah za su kammala a lokacin da aka ayyana.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai