Connect with us

BIDIYO

Da Baiwar Waka Aka Haifeni – Lil_Teemah

Published

on


Matashiyar mawakiyar Hausa hiphop Fateemah Dan Fulani wacce aka fi sani da Lil Teemah aka Efeezy, haifaffiyar garin Kano, wacce ta yi wakar ‘Yar Gwal, kuma tayi wakoki daban-daban kamarsu ‘yar Fulani da kuma Nijeriya kasa Kano jahata. Kwanan nan ya yi wata waka mai taken ‘Yar makaranta wakar tana kunshi da abubuwan duba wa musamman ga mutanen Arewa, da kuma dalibai baki daya. Teemah ya bayyana hakan ne a hirar da suka yi da wakilinmu UMAR MUHSIN CIROMA ga yadda hirar ta kasance:

 

Toh da farko za mu so musan cikakken sunanki?

Suna na Fateemah Isah Dan fulani amma ana kira na da Lil_Teemerh efeedy.

 

Zamu so musan takaitaccen tarihin ki?

An haife ni a ranar 17th March, 1997 a unguwan goron dutse ni haifaffiyar garin Kano ce.

 

Me yasa ake kiranki da wannan sunan bayan Fatima?

lil dai yana nufin little duk wanda ya ganni bazai bani dai dai shekaruna ba,  ai dai ace bana wuce 14 ko 15, shi kuma teemerh nasamu sunan ne daga cikin sunana fateema, sannan shikuma (efeezy) idan mutum ya ganni karan farko sai yayi tunanin ina da efeezy. Amma sai abota ta hada mu sai kaga ba haka bane.

 

Ki yi wa masu karatu bayanin (efeezy) da Hausa?

Eh to shidai efeezy a yadda na dauke shi ba girman kai bane zan iya cewa miskilan ci ko kuma yanga.

 

Me ya ja hankalinki kika tsunduma harkar Hip-Hop?

Abinda yaja hankali na shine ba dan komai ba sai dai nafito na nunawa muta ne masu kurin ciwa a cikin arewa kasar Hausa babu mace da za ta iya raping musamman da Hausa sai dai ‘yan kudu, ni kuma na karyata hakan, tunda zan iya nuna bajimta ta a idon Duniya.

 

To yaushe kika fara waka?

lokacin dana fara rubuta waka tun ina firamari 2 na fara rubuta waka, na kuma fara shiga studio rerawa tun ina JSS 1.

 

Ya zuwa yanzu wakokinki sun kai nawa?

wakokina sun kai 10 amma duka Audio ne babu bideo.

 

Me yasa ba kiyi bidiyo ba?

abin da yasa banyi bidiyo ba banda isasshen karfi ne, amma kwanan nan ina shirin yi.

 

Wakokin na Hausa ne kawai ko da na turanci?

Hausa kawai nake yi bawai dan ba’a iya turancin ba, kuma ina yi ne da alfaharin cewa ni ‘yar Arewa ce, sai yasa bansa turanci.

Kin taba fita zuwa wata jiha ko wata kasa don nuna bajintarki kamar

yadda abokan sana’arki suke yi?

Banje wata kasar ba amma naje jahohi wadanda basu wuce 3 a cikin Arewa.

 

Kina zaune karkashin wata kungiya ne ko zaman kanki kike yi?

Bana karkashin wata kungiya ko daya.

 

To shin waya koya miki waka?

(hhhh) To akwai wadanda ake koyawa suke koya akwai kuma baiwa zan iya cewa tawa baiwa ce babu wanda ya koyamin waka dan akwai wani take dana ke cewa HIP HOP IS MY NEW BORN TOWN.

 

A cikin wakokin ki wanne kika fi so ko yafi birgeki?

duk wakokin da nayi wanda jama’a suka fiso toni ma shi nafiso.

Ko zaki iya gaya mana wasu daga cikin sunayen wakokin da kika yi?

‘YAR MAKARANTA

*JAURO

*JUMMAI MAI KOKON YEN GAYU

*JIGIDA

*’YAR FULANI

*’YAR GWAL

*NIGERIA KASATA KANO GARINA

 

Wani sako wakarki NIGERIA KASA TA take isar wa?

Eh toh sakon da ta isar shine a kan fadace fadacen da ake yi muyi hakuri da juna sannan mu tashi mu hada kan mu, mude na shaye-shaye mu hada kanmu Wazobia da ma ko wace kabila dake nijeriya baki daya.

 

Wani irin kalubale kika fuskanta tun sanda kika fara waka?

Na fiskan ci kalubale sosai musamman a ta gida wajan mahaifiyata mahaifina ‘yan uba mutan gari, akan me ina mace ba Haushiya uwa uba bafulatana ince zan dauki wasu al’adu na wasu kasar waje nace zanyi haka na toshe kunne na rufe idanuna a hankali iyayena suka gane manufata sannan suka barni, dan nayi imani cewa in Allah yace zaka yi abu babu wanda ya isa ya hana, hakuri da juriya da dagiya suke sa mutum yacin ma abin da yake so yayi nasara a kai.

 

To ya kika yi da sauran ‘yan uwan naki?

Suma daga baya sun fahimce ni dan har bani gudun mawa suke akan nayi waka kan kaza ko idan nayi batayi ba sai suce na sake.

 

Wani irin nasarori kika samu daga san da kika fara wakarki kawo yanzu?

Toh Alhamdulillah babu abin da zance wa ubangiji sai dai nace Allah ya karawa Annabi daraja da iya kacin gidan mune suka san ina waka sai studio din da nake waka, amma yanzu Alhamdulillah mutane daban-daban sun sanni itama babbar nasara ce wannan. Dan kuwa koda wanna aka bar ni ya ishe ni tin kaho.

 

Wani irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mawaka?

Shawara ta ga ‘yan uwana shine suyi hakuri a rayuwa abinda hakuri bai ba yarba rashin sa bazai bayar ba.

 

Waye role model dinki?

Nicki Minaj gaskiya.

 

Me yasa kike son Niki Minaj?

sabida ta iya raping sosai, kuma salon ta yana birgeni, kusan in cema tana daya daga cikin wadanda suka samun ra’ayin waka, dan kuwa ina sauraran wakarta sosai.

 

Wani kalan abinci kika fi so?

Da safe naci tuwo miyan kubewa da rana kuma naci shinkafa  da wake.

 

Wani kalan mota kika fi sha’awar hawa?

Matrix

 

Wani kasa kike sha’awar zuwa?

America.

 

Wani shawara zaki ba matasan dake sha’awan fara waka?

Shawarata shine subi iyaye duk abinda suka ce muyi to muyi dan sune cigaban mu a rayuwa sannan mu kare mutuncin kai banda shaye shaye, kuma banda zage-zage ko habaici a waka, muso junan mu gaba daya dan ci gaban Arewa.

 

Daga karshe me zaki cema masoyanki?

Ina mika godiya nag a Allah ma daukaki sarki, daya hada ni da masoyana daga jahohi daban-daban, kuma ina gode masu sosai da sosai musamman iyayena, ‘yan uwa da abokan arziki.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai