Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din Auren Manga

Published

on


Tare Da: Saddika Habib Abba 09097438402 [email protected]

Suna: Auren Manga

Tsara labari: Nazir Adam Salihi

Furodusa: Yakubu Usman

Bada umarni: Falalu A.Dorayi

Kamfani:Sayas Multimedia tare da TJ Multipurpose concept

Jarumai: Falalu A Dorayi, Adam A Zango, Sulaiman Bosho, Hadiza Aliyu Gabon, Yusuf Baban Cinedu, Beatrice Auta, Tandu Kaduna, Ali Artwork, Hajara Usman, Umma Shehu.

Labarin fim din Auren Manga da farkon fim din an nuna abokai guda biyu suna zaune a gidan haya suna tare a daki dayaManga (Falalu A Dorayi) da abokinsa Figo (Adam A Zango) an nuna shi Manga mutumin kirki nesana’arsa ta kanikanci ita ce ta ke zaune da shi a birni,abokin Manga Figo shi sanar’arsa shi dan bun burutu neamma kuma shi ba shi da kirki domin shine ya ke kule kulen matan banza har yana da budurwa Ester (Beatrice Auta) wacce ta ke zuwa dakinsa suna shan sha’aninsu ta re amma duk wannan ba’asan ran Manga ba. wataran an aiko kiran Manga daga kauyensu kuma da ma zai du ba jikin kakansa Baba mai gari yana kwance ba shi da lafiya Manga ya hada tafiyar gabaki daya, kuma damashi kakan na Manga shine mai gari a kauyen na su Manga sannan Manga ma a hannunsa ya ta so har ya ta ho birni domin an nuna shi Manga maraya ne iyayensa sun rasu,shigar Manga ke da wuya cikin garin kai tsaye ya shiga gidansu ya tarar da kanin mahaifinsa da kakan na sa Baba mai gari da kuma kakar Manga (Hajara usman) da wazirin kakan Manga din duk ana zaune ana jiran zuwan Manga,bayan sun gaggaisa Mangaya duba jikin kakannasa a lokacin kanin mahafinsa ya fara yi ma sa fada akan ya ki yin aure bai kamata ace kamar Manga ba sa’anninsa daga mai ‘ya’ya biyu sai mai uku a kauyan amma shiko auranma bai yi ba,Baba mai gari a wurin ya sanya wa Manga dokar bazai yu ace yana jinin sarauta ba wanda watarana ma sarautar hannunsa za ta da wo amma ace bashidaaure ba, a lokacin ya sanya wa Mangasati biyu rak akanya fito da mace a aura masa idan kuma bai fito da ita ba to su za su nema su aura ma sa.

tin daga lokacin suka sanya Manga acikin tunani domin shi ko ‘yanmata ba ya iya kulawa kuma gashi an ce ya samo mace a sati biyu,Manga ya da wo birni ya fara lalube duk wacce ya kula ya ce yana so sai a sami matsala ta ki amsar soyyayar ta sa har ta kai ga ya kula wa ta matar aure ba tare da ya sa ni ba(Umma Shehu) mijinta ya yi masa dankaran duka.ana nan har sati biyu dai ta cika Manga bai fito da mace ba ya koma kauyansu ya shaidawa Baba mai gari cewar bai sami mace ba, Baba mai gari yace to su zasu samar ma sa,a lokacin ya sa ka aka tara wa Manga ‘yan matan garin domin ya zabi wacce ta yi masa a daura musu aure kowacce ta fito sai Manga yace batai masa ba har suka kare kaf ba’asami wacce ta yi ba ana cikin haka sai wani Babban dan giya a garin Alele (Tandu Kaduna) ya kawo ‘yar saBalaraba (Hadiza Gabon) akan idan ta yi a gurin a daura auren a bashi sadakin kawai ya je ya ka she gararin gabansa da su,Manga yana ganin Balaraba ya ce ta yi a wurin aka daura musu aure aka sha shagalin biki daga bisani Manga ya taho da Matarsa birni. suna zuwa birni Balaraba ta fara gida danci iri- iri har ta kai ga wataran sun fita super market da daddare da Manga saboda surutun Balaraba ya sanya Manga ya barta a waje shi kuma ya shiga cikin super market din yana shiga ‘yan sanda sun zo kamen karuwai a titin suka hada da Balaraba aka tafi da ita.Manga yana fitowa yaga bai ganta ba ya tambaya akace an tafi dasupolice station aka kwatan ta masa ya tafi yana zuwa ya fara rantse rantsen matarsa ce ba karuwa ba ce amma D.P.O din (Sulaiman Bosho)saboda wata manufa da ya ke daita ta sanya ya hana Manga belin matarsa ya karyata cewar Balaraba matar Manga ce domin tin a farkon fim din an nuna alakar shi wannan D.P.Odin da matan banza acikin wadanda yake kulawahardaEster budurwar Figo domin ko kamen Karuwai aka je yi yaran D.P.Osu Baban cinedu ba sakamaEster da kawayenta.don shi D.P.O din ma har waya ya kema ta idan za su fitoka me kada tayo wurin da zasu gan ta.

fim din dai har yakare D.P.O din bai yarda ya baiwa Manga belin matarsa Balarababa.

 

Abubuwan birgewa:

1-An samar da wura re wanda suka da ce da labarin.

2- An zuba jarumai da ya wa a fim din kuma dukkansu sun yi kokari wurin isar da sakon.

3- Anyi amfani da kayan aiki masu kyau wurin daukar hotunan fim din.

4- sauti ya fita yanda ya kamata a fim din.

5- mai bada umarnin fim din yayi kokari sosai yanayin yanda aka tafiyar daumarnin fim din.

Kurakurai:

 

1- wasu daga cikin mutanan kauyansu Manga har da kawunsa Kawu alasan suna ta maganar Manga ya fito birni ya yi boko ya koyi yahudanci amma kwata- kwata a rayuwar Manga ta birni ba’a nuna wani abu da za’a ce Manga ya yi karatu na boko ba hasali ma sana’arsa ta baka ni kanci kawai aka nuna yana yi a birni, idan ance ya yi bokon aiki ne bai samu bashiyasa ya ke baka ni kanci to amma akwai lokacin da Manga ya ke fadawa abokinsa Figo cewar ya kira wayarsa bai samu ba ya ji ana yi masa wani turancin banza da shi sam ba ya ganewa,wanda ake fadar ya zo birni ya yi boko shine zai ce haka?

2- An sani cewar kabilanci tsakanin ya ruka ba abune mai kyau ba amma kowacce kabila tana kishin yarenta bata son ko dan ya ya wani ya ai bata ma ta yarenta ba don bata da abin ai batawar ba domin kowacce kabila tana da abin fada amma saboda kishin harshanta ba ta fada wa duniya. fim din Auren Manga fim ne na kabilar hausa amma sai gashi ana nuna rashin kishi na yaren hausa har ana fifita halayyar wasu kabilun aciki masu kyau wanda akace bahaushe ya gaza yin su kamar in daFigo ya ke maganar matan hausawa matsala ce da su gwara Manga ya nemi kabila kuma matan hausawa basu da godiyar Allah sannan ba su iya soyyaya ba da dai sauran ire- iren irin wannan,su ma fa wadancan kabilun da ya ke yaba wa babu yanda za’ayi su kaskantar da na su yaren su ya bawa hausawa kuma fa sai bango ya tsage kadangare ya ke samun damar shiga sannan kowa na yare yana son cigaba domin fina- finan da’akeyi a duniya kowa yarensa ya ke daukakawa amma dakanmu muna nuna rashin kishin yarenmukuma kowa yasani asalin dabi’un bahaushe masu kyau ne babu in da bahaushe zai shiga a duniya ya nuna asalin dabi’arsa ba’ayi son barka ba kawai sai dai za’ace kowacce kabila akwai na kirkinta akwai bata garin ta.

3- An nuna cewar Balaraba ta taba rayuwar birni ta zauna wurin anti din ta daga bisani ta da wo kauye amma sai ga shi abubuwan da ta din ga yi na gida danci lokacin da Manga ya ta ho da ita ya yi yawa sosai tamkar ba ta ma taba zuwa hanyar tashar zuwa birniba ballanta na ace har ta tabayin zaman birni.

4- a farkon fim din an nuna Manga yana amfani da risho a kicin amma lokacin da Manga ya kawo Balaraba birni ya je unguwaya da wo ya tarar dabata yi girki ba sai gashi tana maganar ita ba ta iya amfani da wannan abun girikin ba sa ga shi Manga yana fada mata sai an jono mesa an jona ajikin karfe sannan a kunna masu kallo kowa yasan Gas kenan ake nufi to a yaushe aka canja risho aka sanya gas tunda gidan dai shine kuma kicin din ma shine dai kuma a lokacin da aka hasko kicin din da farko ba’a nuna gas ba risho din nan kawai aka gani.

5- Aciki labarin fim yakamata ace duk abunda za’a sa ko to samar da dalilin sa ko shi an nuna Figo suna tare a gida daya shi da Manga suna abota duk da kowa yasan abokin barawo barawo ne amma an nuna halayyar Manga da ta Figo akwai bam bam ci har fllm din yakareba’a bayyanawa mai kallo dalilin haduwarsu ba tunda sana’arsu ma ba daya bace halayyarsu ma ba daya bace ta ya ya suka hadu? kuma ba’a fadi asalin Figo ba ko da a baki ne shin wanene Figo?

 

Karkarewa:

Fim din ya nishadantar, amma kuma an karkasa labarin kashi-kashi, domin zaren labarin bai ta fi kai tsaye ba.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

manyan-labarai