Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Hanyoyin Sahara: Ko Gwamnatin Gaidam Ta Bunkasa Tattalin Arzikin Arewacin Yobe

Published

on


Daga Muhammad Maitela, Damaturu

 Karancin hanyoyin mota a arewacin jihar Yobe, wanda yaki ne dake karkashin mamayar rairayin hamada, matsala ce wadda tayi kamari sosai tare da jawo karancin abubuwan more rayuwa da zirga-zirgar kayan amfanin noma da kasuwanci a yankin, a cikin shekaru aru-aru. Matsala ce wadda tayi kama da yankin da aka manta dashi dangane da samun cikakken kulawar gwamnatocin baya, abinda ya zama tarnaki ga al’amurran ci gaban tattalin arziki da walwalar jama’ar arewacin jihar.

Yankin arewacin Yobe, wadnda wannan matsala ta gurgusowar hamada ta ta’azzara a cikin sa, ya kunshi kananan hukumomin Gaidam da Yunusari da Yusufari da Karasuwa tare da Machina. Har wala yau kuma, baya ga karancin hanyoyi, yanki ne wanda ya dade yana fama da koma baya idan an kwatamta shi da sauran yankunan jihar.

Gwamnatin jihar Yobe a karkashin Alhaji Ibrahim Gaidam ta yi la’akari da wannan hali na koma baya da yankin ya dade yana fama dashi, tare da mayar da hankalin ta wajen farfado dashi inda ta gina hanyoyin mota daban-daban a tsakiyar rairayin hamadar, domin saukaka wahalhalun da jama’ar wannan yankin ke fuskanta. Musamman hanyar mota mai matukar muhimmanci kuma mai tsawon kilo mita dari uku (300); wadda ta ratsa tsakiyar rairayin hamada. Bugu da kari kuma wadda ta hada hancin garuruwa da kauyuka masu yawa a arewacin Yobe, kana da hade kan iyakar Nijeriya da jamhuriyar Nijar.

Gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam ta taka rawar gani tare da share hawayen al’ummar wannan yankin da a jihar Yobe baki daya ta dalilin samar da wannan hanya wadda a baya ake kallon sa da abu mai kamar wuya, saboda yadda yankin ya kasance a tsakiyar hamada. Haka zalika, wanda a baya ya dakushe aniyar gina hanyar mota ta dalilin hamada wanda gina hanyar mota a sahara zai jawo kashe makudan kudi maras adadi.

Muhimman hanyoyin mota a tsakiyar rairayin hamada wadanda gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam ta gina da dan kason da take samu, sun kunshi babbar hanya mai tazarar kilo mita 300 wadda ta tashi daga daga Kanamma ta doshi Machina, wadda aikin ta ke ci gaba da gudana. Kana da takwarorin ta da suka hada da ta Geidam zuwa Bukarti da hanyar Bayamari zuwa Yunusari, sai wadda ta tashi daga Gashua zuwa Yusufari. Sauran sune hanyar nan wadda ta taso daga garin Bukartinnyamma zuwa Karasuwa da ta Geidam zuwa Kanamma, da sauran su, wadanda gwamnatin jihar Yobe ta gina.

 

Yayin da gwamnatocin da suka shude; na soja ko na farar hula, ba tare da tabuka wani abin a zo a gani ba a bangaren, hobbasar da sai a lokacin mulkin Alhaji Ibrahim Gaidam, hakar al’ummar arewacin Yobe ta cimma ruwa. Duk da ko yadda hankoron tsohuwar gwamnatin baya ta kasa cimma muradin ; wanda ana a iya cewa bai taka kara ya karya ba, matsalar da ta ci gaba da kasancewa al-kakai a koma bayan yankin ta bangaren hanyoyin mota da a ci gaban tattalin arziki.

Bangaren arewacin jihar Yobe yanki ne wanda yake da tazarar kimanin kilo mita 300 daga jihar Borno, mai iyaka da jihar Jigawa ta gabas tare da hada kan iyaka guda da jamhuriyar Nijar. Yanki ne wanda kusan ana iya cewa; wanda a shekarun baya idan ka zagaya shi, bashi da wata babbar hanyar mota ta a zo a gani, wadda ta sada garuruwan yankin. Yankin arewacin Yobe mai makwabtaka da Nijar ta garin Meine-Soroa wadda ta hada shi da manyan garuruwan kasar irin su Ngegeme da Diffa da Zander, da makamantan su, wajen gudanar da kasuwanci da zirga-zirgar jama’a, a tsakani.

A hannu guda kuma, ta dalilin yadda a cikin shekaru masu yawa wadanda a cikin su gwamnatin tarayya ta nuna halin ko oho, dangane da sha’anin bunkasa al’amurran ci gaban tattalin arzikin yankin, a karancin hanyoyin mota da more rayuwa. Yayin da sai a zuwan gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam ne ya zuba wa zafin wannan matsala ruwa, halin da ya canja fasalin rayuwar al’ummar da ke zaune a wannan yankin mai makwabtaka da jamhuriyar Nijar, zuwa hali mai kyau.

Zancen da ake yi a yanzu haka, aikin wannan muhimmiyar hanaya mai tazarar kilo mita 300 wadda gwamnatin jihar Yobe ta bayar, yana ci gaba da gudana, kuma an kammala sama da kaso 50 cikin dari na aikin. Wannan namijin kokarin babban tarihi, na gina wannan hanya wadda ta ratsa tsakiyar hamada karkashin gwamna Gaidam ya kafa. Hanyar wadda ta taso daga garin Kanamma ta shigo Kafiya, zuwa garin Yunusari, ta shiga Yusufari. Bugu da kari kuma, hanyar ta tashi daga Yusufari zuwa Kumaganam ta fada garin Machina; wanda ake sa ran kammala shi nan bada jimawa ba.

Bisa ga wannan kuma, kawowa yanzu, daga garin Kanamma zuwa Kafiya, ta biyo Yunusari ta fado Yusufari, an riga an kammala ta, wadda kuma tsawon hanyar ya zarta kilo mita 150. Tare da wannan kuma, garuruwa da kauyuka da dama a wannan yankin sun matso daf-da hanyar mota, wanda kuma hakan ya saukaka musu wahalhalun sufuri da jama’a ke fama dashi tare da kayan su. Bugu da kari kuma, halin da ake ciki yanzu, jama’a suna iya amfani da kowanne nau’i na motocin hawa da suka ga dama, tare da dakon kaya daga yankin nasu zuwa cikin jamhuriyar Nijar kuma a cikin kwanciyar hankali.

Samar da wadannan hanyoyin a cikin wannan farfajiyar rairayin hamada ya canja fasalin rayuwar jama’a daga tsohuwar al’adar amfani da jakuna da dawakai ko rakuma ta fuskar zirga-zirgar al’umma da kayan su tare da maye gurbin su da ci gaban zamani da habaka yanayin tattalin arzikin jama’ar da ke zaune a yankin hamadar arewacin Yobe.

LEADERSHIPA Yau ta jiyo ra’ayoyin jama’a da dama a wannan yanki na arewacin jihar Yobe dangane da alfanun waddannan hanyoyi, wajen bunkasa tattalin arziki da sufuri. Yayin da suke ala-san-barka da fatan alheri ga Gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam.

Malam Baba Alkali, Yusufari ya fara da bayyana ra’ayin sa da cewa” a shekarun baya, kamar gwamnatoci sun manta da wannan yanki namu. Amma alhamdulillah, Allah ya kawo muna Gawamna Alhaji Ibrahim Gaidam, inda ya tuna samu kuma ya share muna hawayen mu bisa ga abinda ya fi samun mu a wannan yanki, shi ne matsalar hanyar mota da abubuwan more rayuwa. Rayuwa ta canja daga kunci zuwa walwala da farin ciki, sai yanzu muka gane gwamnati ta san da zaman mu”. Inji shi.

“Yanzu gashi a cikin sauki muke gudanar da harkokin sufurin mu da kasuwanci tare da dauko kayan amfanin gona, ta dalilin wadannan hanyoyin mota kuma wadanda suka ratsa kusan manyan kauyukan mu. Bugu da kari kuma, sun taimaka wajen bamu zarafin sada zumunci tsanin wannan gari da wancan; sabanin a da. Ribar wadannan hanyoyi ba zasu kirgu a cikin dan kankanin lokaci ba, sun taimaka wajen habaka tattalin arzikin jama’ar yankin mu”. Baba Alkali.

Shima Umar Abdullahi, mazunin garin Yunusari ya shaidar da cewa, baya ga yadda wadannan hanyoyin mota da gwamnatin Yobe ta gida zasu taimka wajen saukaka zirga-zirgar jama’a da kayan su. Haka kuma sun bude kafar samar da ayyukan yi ga matasan wannan yanki, inda ya ce yanzu haka matasa da dama sun mallaki motocin haya da gudanar da kasuwancin dabbobi da kayan amfanin gona daga yankin zuwa wasu jihohin kasar nan. Ya ce wannan ya jawo kwalliya ta biya kudin sabulu wajen samun sana’a da dogaro da kai ga matasan.

Duk inda ka shiga a cikin wadannan garuruwa, wadanda wannan hanyoyin suka bi ta cikin su, sai annashuwa suke tare da jinjina ga gwamnatin jihar Yobe tare da bayyana cewa ta share musu hawayen su, da gaskata mafarkin da suka dade suna yi “ba zamu taba mantawa da wannan karramawa da Alhaji Ibrahim Gaidam ya nuna muna ba, ka kalli yadda gina wadannan hanyoyin mota suka daga kimar mu suka mayar da wannan yanki kamar kowanne yanki a kasar nan. Wanda a baya idan ba lafiya sai dai a dauki mutum a jaki ko doki da rakumi; idan nakuda ta ta’azzara ga mata wanda har sai an kai asibiti, dole sai dora ta a jaki sannan a kai inda asibiti take. Amma yanzu komai ya warke(na rasa abinda zan fada maka)! Inji wani dattijo Baba Ari Bukar a garin Kachalla.

A hannu guda kuma, baya ga kyautauwar lamurran sufuri da kasuwanci kana da yadda manoman yankin ke dakon kayàn amfanin gonakin su cikin sauki. Bugu da kari kuma, akwai bunkasar wasu bangarori na jin-dadin al’umma da suke gudana fiye da a baya; kamar yadda sha’anin kiwon lafiya da ilimi suma suka bunkasa ta dalilin samar da wadannan hanyoyin mota. Yayin da a baya malaman makarantu da ma’aikatan kiwon lafiya ke dari-darin shiga yankin, saboda wahalar abin hawa, amma yanzu duk wannan ya kau.

Malam Kaumi Ali, Yusufari ya bayyana cewa, a shekarun baya rashin hanyoyin mota ta dakushe al’amurran kiwon lafiya a yankin, yanayin da ke jawo mutuwar mata da kananan yara “a shekarun baya, jama’ar wannan yanki suna shan bakar wahala wajen daukar mata masu ciki ko tsuffi zuwa asibitoci; ta amfani da jakuna ko dawaki da rakuma. Amma yanzu gashi Allah ya kawo muna sauki ta dalilin wannan bawan Allah; Alhaji Ibrahim Gaidam, ya gina muna hanyoyin mota, kuma a cikin kankanen lokaci zamu dauki majinyatan mu zuwa asibitoci ba tare da wahala ba. Kuma wannan ya rage yawan mutuwar mata da kananan yara a wannan yanki namu dama a jihar Yobe baki daya.” Ya bayyana.

Wadannan hanyoyin mota sun karfafa gwiwa wajen bunkasa kananan sana’o’i a yankin kuma wannan ya samu ne ta hanyar tururuwar yan kasuwa dake zuwa daga sassan kasar nan; kusa da nesa, wadanda ke zuwa su baje hajojin su, tare da shiga cikin kauyuka a yankin. Sabanin a shekarun baya wanda abin ba a cewa komai.

Gwamna Gaidam ya sha nanata cewa gwamnatin sa ba zata taba yin kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kammala wadannan hanyoyin mota, nan da zuwa karshen shekarar 2019. Ya bayyana cewar wannan kuma yana da nasaba da muhimmancin hanyoyin ta fuskar habaka tattalin arzikin jama’ar yankin, ya sha alwashin cewa, an samu ci gaba a sha’anin matsin tattalin arziki wanda kasar nan ke watangarereniya a ciki, zai ci gaba da karasa sauran aikin hanyar daga Yusufari zuwa Kumaganam ta fada garin Machina, ya ce domin suma su san ana damawa da su.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI