Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Lambar BVN: Bankuna Na Yi Wa Yaƙi Da Rashawa Zagon Ƙasa –Minista

Published

on


Daga Idris Aliyu Daudawa

Gwamnatin tarayya tare da Babban Alƙalin Gwamnati kuma Ministan shari’a Abubakar Malami (SAN) sun yi zargin cewa Bankuna 19 na da laifi saboda ƙi bin umarnin Kotu akan lambar ta tantance asusun ajiya, wannan yananuna ke nan, su Bankunan suna kawo zagon ƙasa a shirin da gawamnatin tarayya ta ke yi na yaƙi da karɓar rashawa.

Ita dai kotun watanda ya gabata ne ta bada umarni na a rufe dukkan asusun ajiyar da ba ayi ma shi ita wannan lambar ba, mai nuna haƙiƙanin wanda ke da shi asusun ajiyar.

Gwamnati ita da Ministan shari’a sun yi wannan zargin ne, akan wani kare kan da suka yi, saboda ƙarar da su Bankunan suka shigar, inda suke ƙalubalantar ita kotun akan matakin da ta ɗauka cewar ya sab aba tada ani hurumi na saurara  ita wannan ƙarar da ke gabanta.

A wata ƙara  wadda Usman Dakas ya shigar a madadin gwamnatin tarayya da kuma Babban Lauyan Gwamnati, ya ce, ‘’Su Bankunan a gaskiya wannan matakin da suka ya nuna  a fili, ba suna goyon bayan, shi umarin da kotun ta bayar,da kuma ta faɗi  a rufe asusun ajiyar da ba wannan lambar ba, wannan ya nuna suna nema ne  a gurgunta shirin da Gwamnatin tarayyar take yi, na yaƙi da masu ƙoƙarin kawo ma tattalin arzikin ƙasa tu’annafi. Wannan shiri kuma shi ne  wanda, za a tabbatar da masu ajiyar kuɗaɗensu a Bankunan.

Lauyan gwamnati Mista Danjuma Tyoden shi ma ya bada nashi baa sin ne a wata ƙarar da ya shigar, wanda shi ma yana ƙalubalantar matakin da Bankunan suka ɗauka .

Ya cigaba da cewara su Bankunan ba kawai sun kao ma gwmnatin tarayya cikas bane, wanda kuma tsarin mulki ya bata dama, ta yi maganin duk aɗansu al’amuran da suka shafi karɓar rashawa da cin hanci. Amma duk da hakan suna nuna  rashin jin daɗinsu ne yadda aka nuna rashin biyayya ga umarnin kotu, wannan yana nuna ke nan zasu cigaba da mu’amala da waɗannan Bankunan ta yadda nan gaba, suna iya amfdani da asusun ajiyar da basu da wannan lambar, su yi kasuwanci da kuɗaɗen, daga ƙarshe kuma su Bankunan suce sun samu gaggarumar riba musamman ma idan ƙarshen shekara ya yi.

Tyoden ya ƙara jaddada cewar su Bankunan da suka kai wannan ƙarar sun yi ne domin kawo cikas a wani tsari na Gwamnati wanda su a ganinsu , hakan bata yi masu daɗi ba, ina son jama’a su gane cewar tsarin mulkin ƙasa ne ya ba ita gwamnati dama ta kawo cikas ga duk wani shiri da ake tunanin da akwai lauje cikin naɗi. Wannan maganar lambar masu asusan ajiya Babban Bankin ƙasa ne ya bada umarni ko ne mai asusun ajiya , to ya yi ƙoƙari ya gaya samu ita lambar.Wadda kuma ita Bankin da mutum yake da asusun ajiya can yake zuwa ake buɗe ma shi.

Shi wannan al’amari yana da ɗaure kai saboda kuwa a lokacin da su Bankuna suke farin ciki, na ba zasu bar masu asusun da ba, lambar su riƙa amfani da su, amma kauma duk da haka suna buƙatar su shugabannin riƙo, da su ba Bankuna umarni na su bayyana sunayen masu ajiyar, a kori ƙarar ko kuma a soke ta.

Gwamnatin ta nuna rashin jin daɗinta  na yadda su Bankunan suka ƙi bin umarnin kotun na cewar su bayyanasunayen ajiyar asusun da ba wannan lambar ajiyar, saboda idan suka yi hakan wani zargin da ake masu zai ragu.

Takardar da Gwamnati ta rubuta tana buƙatar cewar su Bankuna su buga sunayen masu ajiyar da ba, wannan lambar, domin idan aka yi haka , duk wata maganar zargin juna a wuce wurin.

Maganar gaskiya me yasa me yasa suka ɓoye takardar umarnin da kotu ta basu na cewar, su bayyana sunayen idan dai har ba suna tsoron wani abu ba.

Ya cigaba da bayanin cewar suasusun ajiyar kuɗaɗen da basu da lambar ai ba na Bankunan ba ne, don haka me kuma yasa yanzu suke da shakkun, da kuma nuna abin ya dame su fiye da waɗanda ke da kuɗaɗen nan, ai an bada wannan umarnin na buga sunayen masu asusun ajiyar da ba lambar.

Ita gwamnati tana iƙrarin cewar ai asusunajiyar da babu lambar da ake buƙata ai na abokan hulɗa da bankin ne, su kuma ne yafi dacewa su yi wani ƙorafi na an danne masu hakki, idan da shi ma.

Abin da akwai matuƙar ɗaure kai saboda Bankuna sun eke cewar su ne ya kamata su bi sharuɗɗan da doka ta shimfiɗa, yanzu kuma sune ke ƙoƙarin kare masu ajiya, wanda hakkin masu ajiyar ne.

Takardar kotu wadda ta ba gwamnati ai cewa tayi ‘’ Ko shakka babu abin yana da ban mamaki wai yanzu Bankuna ne suke nuna rashin jin daɗinsu akan umarnin kotu, wadda tace masu ta bayyana sunayen masu ajiya ba tare da lambar ba, ta asusun ajiya, yanzukuma abinya yi masu ciwo ne sune kuma yanzu kai kare masu ajiya. Wannan faya taka dokar Babban Bankin ƙasa, wadda kuma tana daga cikin tanade tanaden na kasan buƙatun abokan hulɗarka.

Ko shakka babu Bankuna sune waɗanda aka sani da sai sun amince da al’amaringaskiya, shi yasa ma wasu ke yarda, su tafi tare da su, idan kuma maganar faɗa da aikata laifuka ta taso, su bayyana mutanen da suke da shakku akan su, ba kuma dole sai sun samu garaɓasa ba, kamar daga  wurin mutumin da ake da shakkun yadda ya tara dukiyar shi. Wanda idan hakan ne lalle ya aikata laifi yana dai dai, da wanda ya kawo ya ajiye mai kuɗaɗen sata.

Bugu da ƙari gwamnati ta gano laifin su Bankunan wato inda suke cewar takardar ƙara da gwamnatin tarayya ta gabatar, a ƙarƙashin sashe na 17(1) (da kuma ƙaramin sashe na ɗaya) wannan al’amari Hukumar EFCC ce zata iya yin wani abu dangane da hakan.

Babban Alƙalin Gwamnatida gwamnatin tarayya sun ƙalubalanci cewar, doka bata hana masu ba, su da sauran Hukumomi na gwamnati waɗanda aka ɗora ma alhakin yaɗi da al’amuran da suka shafi karɓar rashawa da cin hanci, yin aiki kamar yadda doka ta tanada.

Mai shari’a Nnamdi Dimgba ranar 17 ga watan Oktoba ne na wannan shekara, bisa ga la’akarin da yayi da takardar gwamnatin tarayya, an ba Bankunan 19 da Babban Bankin ƙasa, da cewar su bayyana sunayen asusun ajiya,  da basu da lambar,  da kuma ko nawa ne ya rage a asusun.

Ita ma kotun har ila yau ta ba Bankunan umarni na su bayyana cikakkun bayanai na dukkan waɗannan asusun ajiyar, waɗanda ke da kuɗaɗen, da kuma duk waɗansu abubuwan da ake buƙata.

Hakanan ma akwai wata doka da ta umarci Bankunan su rufe dukkan waɗannan asusun ajiyar, da kuma dakatar da duk kuɗaɗen da za a iya fitarwa, ko kuma shigarwa, har sai an kammala sauraren, wata ƙarar da aka shigar mai neman, da duk a riƙe wasu ragowar kuɗaɗe na asusun ajiya na gwamnatin tarayya.

Kotun dai ata sake umartar Babban Bankin ƙasa da kuma wata Hukuma mai gyara hulɗa tsakanin Banki da Banki, da su sake nazarin dukkan waɗansu bayanai waɗanda Bankuna 19 suka gabatar, a ƙarar da suka shigar, a cikin kwanaki bakwai( 7) na  umarnin da ka bada. Bugu da ƙari an umarci su Bankunan da su buga sunayen asusun ajiye waɗanda basu da lambar, a Jaridar ƙasa, watakila yin hakan zai iya sa wasu su nuna sha’awarsu dangane da asusun ajiyar.

Amma kuma maimakon abi umarnin kotun kamar yadda aka buƙata, sai su Bankunan kuma suka ya fi dacewa da su shigar da ƙara, wannan ya nuna ke nan basu amince da wannan umarnin na kotu ba, sai ma suke tambaya akan cancantar umarnin da kotun ta basu.

Bankunan ta hanyar Lauyoyinsu waɗanda manyan masu shari’a na ƙasa Messrs Usoro Babatunde Fagbohunlu  da kuma  Adeniyi  Adegbonmire sun buƙaci sun shigar da ƙarar, inda kuma suka buƙaci kotun data, kar ta saurari ƙarar, ko ta kore ta, bayan nan kuma ayi amfani da matakin da aka ɗauka ranar 17 ga  Oktoba.

Mai shari’a Dimgba a lokacin da aka yi wancan zaman ranar 15 ga Nuwamba, kamar dai yadda aka bada umarni ranar 17 ga Oktoba

Dokar ta ce a wallafa sunaye waɗanda asusun ajiya amma kuma ba ita wannan lambar,a kuma sake buɗe nanbar asusun  al’amarin da ake danganta shi da akwai matsala bayan da aka bada umarnin.

Hakanan Alƙalin ya soke umarnin da ya bada mai lamba 5, wanda ya bada umarni ga shugabannin riƙo akan, al’amarin da ya shafi, duk waɗansu kuɗin ajiyar da basu da lambar, har sai idan an kamala sauraren ƙarar da aka shigar.

Waɗanda suka shigar da ƙarada suka haɗa da gwamnatin tarayya, Babban Alƙalin Gwamnatikuma Ministan shari’a na ƙasa Abubakar Malami an wakilce su lokacin da, aka saurari ƙara wanda ya wakilce su  shi ne Mista Joseph Tobi, sai kuma Bankunan 19 Mista A deniyi Adegbonmire shi ne ya wakilce su.

Babban Bankin ƙasa ne kaɗai sai kuma ɗanda aka sa sunansu a ƙarar, su ba wani lauyan da ya wakilcesu, mai shari’a Dimgba ya ɗaga sauraren shari’ar har sai 11 ga watan Disamba.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI