Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Agbura: Garin Da Aka Fara Samun Cutar Ƙyandar Biri

Published

on


Daga Sabo Ahmad

Garin Agbura da ke Jihar Bayelsa, shi ne gari na farko da ake da tabbacin cewa, an fara samun ɓarkewar annobar Ƙyandar Biri a faɗin tarayyar Nijeriya. Wannan rahoto ne na musamman a kan  dalilin da ya sa aka danganta samuwar cutar da wannan gari.

Yara na ta yin wasanni, ba tare da lura ba. Manya na ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu ba tare da wata matsala ba. Maƙwabta na ta hidimarsu ranar Asabar ba tare da tunanin abin da ya faru ba, wanda ya ja hankalin jama’a kan garin Agbura ba; wani babban gari ne a yankin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Sunan garin ya fito fili ne lokacin da aka yi ta yayata cewa, nan ne gari na farko da aka fara samun ƙwayar cutar Ƙyandar biri.

Saboda haka mazna wani gari wanda ke kusa da garin Otuokpoti, da ke ƙaramar hukumar Ogbia, na gudun baƙi.

Duk da haka, bai hana shigowar baƙin ba, musamman ma’aikatan lafiya da jami’an gwamnati, waɗanda ke zuwa domin yin bincike a kan labarin da ake yaɗa wa na ɓullar Ƙyandar biri a wannan gari.

Masana sun bayyana cewa, Ƙyandar biri, cuta ce da ake iya ɗaukarta ta hanyar idan birin da ke da cutar ya yi cizo, ko ta  hulɗa da birin da ke da cutar, ko cin naman dajin da ba a gyara shi sosai ba, wasu daga cikin mutanen garin sun yi imani da cewa, naman daji wata garaɓasa ce da suke da ita a yankin.

Saboda haka, wani mazaunin garin, Mista Egba Jonathan, ya gaya wa jaridar Leadership A YAU cewa, wata yarinya ce ‘yar sakandire ta kawo musu cutar daga wani guri.

Ya ce, yarinyar na cin naman daji a ƙauyensu da ke kudu-maso-gabashin ƙasar nan, alamun cutar sun fara bayyana a jiknta lokacin da ta dawo garin Agbura.

Shi ma Jonathan ɗan asalin garin wanda ya bayyana cewa, ba su taɓa ganin wannan cuta a garin na su ba, sai lokacin da ta kwantar da wani yaro, wanda suka yi zaton ƙyanda ce kawai, amma daga baya bincike ya gano cewa, wata annoba ce ta faɗo wa garin.

Ya ci gaba da cewa, daga baya mutanen garin suka fara jin cewa, yaron ya kamu ne da cutar Ƙyandar biri, daga nan ma’aikatan asibiti suka ɗauke shi tare da wani ƙanensa ɗan shekara bakwai wanda shi ma ya kamu da cutar.

Jonathan ya ce, “mutanen garin suna ganin abin kamar wasa, lokacin da jami’an lafiya suka ɗauki yaran, suka kai su guri na musamman da aka keɓe a asibitin koyarwa na jami’ar Neja Delta, da ke Okolobiri don ci gaba da kula wa da lafiyarsu. Bayan sun samu sauƙi na samu labarin sun dawo gida, amma na kasa zuwa in gaishe su, saboda tsoron kada ni ma in kamu da wannan cuta’’in ji shi.

Haka kuma wata mazauniyar garin da ke Unity Street, kusa da wata sakandire inda aka ɗauki bayanin masu cutar, ta bayar da labarin da ya sha bamban kan yadda cutar ta fara ɓulla a wannan gari.

Matar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta ta ce, yaran da suka fara kamu wa da wannan cutar kullum tana ganinsu suna wasa da birin maƙwabcinsu. “Wani lokaci ma nakan gan su har suna kis da birin, ina ganin a nan ne suka ɗauki wannan cutar” in ji ta.

“Duk da wannan annoba da ke faruwa a garin ba mu yi hijira ba, muna nan zaune kamar yadda kake gani, nan muke ci gaba da rayuwarmu. Ko iyayen yaran ma sun tafi wajen aiki, uwar yaran na sayar da abinci, shi kuma uban na aiki a Yenagowa.

“Jami’an kula da lafiya na yawan shigo wa wannan gari, ina tabbatar maka da cewa,jami’an lafiyar sun ɗauke wannan birin, domin tun da abin ya faru muka daina ganinsa.’’

Ta ce, da farko ba su ɗauka cewa, wannan babbar mtsala ba ce, saboda suna tsammanin kawai cutar ƙyanda ce irin wadda aka saba da ita, sai daga baya suka gane wannan wata daban ce, wadda ta fi wadda suka sani haɗari.

“Mun ƙara tsorata da wannan cuta lokacin da muka dinga ganin ma’aikatan lafiya na shigo wa wannan gari, kuma muna ta jin ana gargaɗi a kan hanyoyin da suka kamata mu bi domin guje wa kamu wa da wannan cutar a gidajen rediyo.

“Ta ce, mun samu labarin cewa, iyayen yaran, da ke tare da su, ba su kamu da cutar ba, ballantana mu da ba ma tare, saboda haka tsoron me za mu ji?  Abin da ya kamata mu yi shi ne, mu kiyaye, kamar yadda  jami’an kula da lafiya ke faɗakar da mu.

Wasu  mazauna Unity Street, sun shaida wa Leadership A YAU, cewa ba za su bar yankin ba duk da wannan annoba da ke faruwa.

Sai dai sun bayyana cewa, za su nisanta kansu daga zuwa gidan da yaran suke, duk da cewa sun samu lafiya, saboda faragabar da suke da ita na yin hulɗa da su a halin yanzu.

Wakilinmu wanda ya ziyar gidan da yaran suke, bai samu damar magana da ko mutum ɗaya daga cikin iyalan yaran ba. Ɗaya daga cikin mazauna gida ya koma cikin gidan a guje, ya kuma jawo ƙofa ya rufe lokacin da ya ga wakilinmu zai shiga gidan.

Babu wanda ya fito waje, har lokacin da wakilinmu ya bar ƙofar gidan da misalign ƙarfe 6ny.

Sai dai an ji wasu daga cikin mutanen gidan da suka raɓe a wata kwana suna magana ƙasa-ƙasa kan abin da ke faru wa.

Wani mazaunin gidan wanda ake yi masa laƙabi da King mai sayar da naman daji da giya, ya ce, mutane ba sa sayen naman daji a wajensa  tun lokacin da wannann abu ya faru, saboda haka, kasuwarsu ta yi ƙasa sosai.

“Ba na iya ciwo kansu don su sa yi naman, saboda wannan abu, saboda haka, ni ma na dakatar da sayen naman, har sai lokacin da komai ya zama daidai, sannan in ci gaba da sana’ar ta wa, amma dai a yanzu na dakata,’’in ji shi.

Bayan wannan kuma mazauana garin na guje wa yin hannu da cinkoson jama’a, saboda tsoron kamu wa da cutar. Daga ranar Juma’ar da ta gabata an samu mutum goma sha uku da suka kamu da wannan cuta.

Hukumomi sun bayyana cewa, an samu nasarar warkar da wani likita da wani yaro ɗan shekara 11  da suka kamu da cutar a asibitin koyarwa na jami’ar Neja Delta da ke Okolobiri.

Kwamishinan lafiya Ebitimitula Etebu. Ne ya bayar da wannan shawarar ta a guji yin hannun da haɗa jiki, domin guje wa kamu wa da wannan cuta.

Haka kuma kwamishinan ya jaddada muhimmancin wanke hannu sosai kafin a ci abinci da kuma tsaftace dukkan jiki da muhalli, don daƙile ci gaba da yaɗuwar cutar.

Etebu ya ci gaba da cewa, gwamnati na iya ƙoƙarinta na ganin ta kawo ƙarshen wannan annoba da ke da barazana ga rayukan al’ummar wannan yanki.

Ya ce, duk da cewar an samu wannan cutar a jikin biri ne, amma ana iya samun ta a jikin sauran namun daji irin su ɓera da kurege.

“Ana iya kamu wa da cutar daga kowane naman daji, ana kiranta Ƙyandar biri ne saboda daga biri aka fara gano ta.

A ƙarshe, kwamishinan ya ce,an yi wannan binciken a kan cutar a Agbura, in da wani mutum ya mutu sakamakon cin naman biri, sannan aka ga ƙuraje na feso wa wasu mutanen garin waɗanda ba a saba ganinsu ba.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI