Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yan Jarida Da Fursunoni Za Su Kaɗa Ƙuri’a Kafin Ranar Zaɓe A 2019

Published

on


Daga Yusuf Shuaibu

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce tana shirye-shiryen tabbatar da cewa ‘yan jarida, jami’an tsaro, da masu sa ido a zaɓe, da ‘yan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam da ‘yan fursuna sun kaɗa ƙuri’a kafin ranar zaɓe a shekarar 2019.

Hukumar ta kuma ce za ta ɗauki ma’aikata miliyan ɗaya su gudanar da zaɓan 2019.

Shugaban hukumar zaɓan Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana hake a Abuja a tsakiyar makon nan, a lokacin da yake ba da ba’asi a gaban kwamitin Majalisar Wakilai da ke kula dda harkokin zaɓe.

Ya tabbatar da cewa hukumarsa za ta bi duk wani hanyoyin da za a yi zaɓe a cikin lokaci kamar yadda ake yi a ƙasashen da suka ci gaba.

Yakubu ya bayyana cewa, Hukumar INEC ta lura cewa jami’an tsaro, ‘yan jaridu da kuma masu sa ido a zaɓe ba su samun damar kaɗa ƙuri’a a lokutan zaɓe saboda suna aikin sa ido da tsokaci a yayin gudanar da zaɓen.

A kan ma’aikatan da za su gudanar da zaɓen kuwa, shugaban hukumar ya ce, hukumar tana da  ma’aikata dubu 16 wanda sun yi ƙaranci, shi ya sa yake shafar ayyukan zaɓe.

Yakubu ya bayyana cewa, a 2015 hukumar ta ɗauki ma’aikata na wacin gadi guda 750,000, wanda ya kamata a kara gudanar da zaɓan yadda ya kamata.

Da yake warware mishkilar na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a, Farfesa Yakubu y ace matsalar da aka fuskanta a baya ba asali ta na’urar b ace, illa rashin ƙwarewar ma’aikatan da suka yi aiki da ita. Don haka y ace hukumar ta duƙufa sosai wajen inganta na’urar da sauran abubuwan da suka wajaba da za su tabbatar da samun nasarar aikin.

Dangane da ranar da za a kammala aikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a kuwa, Shugaban INEC y ace doka ta ba da dama a yi aikin rajistar har zuwa aƙalla ana saura wata biyu a yi zaɓe. Y ace hukumar ta fara aikin da wuri ne domi9n tabbatar da cewa duk wanda ya cancanci zaɓe an masa rajista domin ya samu damar yin zaɓe a matsayinsa na ɗanƙasa.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI