Connect with us

WASANNI

Nijeriya Ce Ta Biyar A Afirka Sannan Kuma Ta 41 A Duniya

Published

on


Daga Abba Ibrahim Wada

Tawagar yan wasan super eagles ta kasa itace ta biyar a nahiyar Afirka sannan kuma itace ta 41 a duniya kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ta bayyana a jiya.

A watan daya gabata dai nijeriya ce ta 44 a duniya kuma ta biyar a duniya wanda hakan yake nufin ansamu cigaba a wannan watan bayan ƙasar ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya wanda za’ayi a ƙasar rasha bayan ta doke ƙasar Zambia.

Nijeriya dai tasamu maki 721 a wannan watan inda a watan daya gabata da samu maki 696 kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta bayyana.

Ƙasar Tunisia itace ta daya a nahiyar Afirka inda take ta 28  a duniya bayan data hada maki 834 sai ƙasar masar, wadda take matsayi na biyu inda take matsayi na 30 bayan data hada maki 818.

Ƙasar Senegal ce ta uku a Afirka inda take mataki na 32 a duniya sai congo a mataki na hudu a Afirka sannan take mataki na 35 a duniya.

Ƙasar jamus ce ta daya a duniya sai Brazil a matsayi na biyu. Portugal har yanzu tana matsayi na uku sai Argentina a matsayi na hudu yayinda Belguim take mataki na biyar.

Ƙasar Poland ce a matsayi na shida sai faransa a marsayi na bakwai.

Shugaban magoya bayan yan wasan super eagles ta ƙasa, Mista Osita Okeke ya ce,  nasarar da nijeriya tasamu ne a wasan data fafata da ƙasar Zambia yasa ta ƙara samun matsayi inda ya ce,  yana fatan yan wasan ƙasar zasu cigaba da buga abin azo agani domin fitar da ƙasar daga kunya.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI