Connect with us

LABARAI

Yaƙi Da Boko Haram: Rundunar Sojan Sama Ta Buɗe Sabon Sansani A Monguno

Published

on


Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Rundunar sojan saman Nijeriya (Nigerian Air Force) ta ɗauki matakin kafa Sabon sansani domin kai hare-hare kan sansanoni daban daban na ƙungiyar boko haram a garin Mongunu dake arewacin jihar Borno.

Shugaban Rundunar Operation Lafiya Dole Air Kwamanda Tajuddeen Oladele Yusuf, ya bayyana haka ranar talata a Yola lokacin wani taron ‘yan jaridu na wata uku-uku da rundunar ke gabatarwa.

Yace akwai dabaru da kwarewar da rundunar ta ke dashi, wanda zai bata daman kaiwa ga sansanonin ƙungiyar boko haram da cimmasu dama wuyar tantancewa sakamakon yanayin sararin samaniyar yankin.

Shugaban Rundunar ya kuma yaba nasarorin da ya rundunar operation Ruwan Wuta ta samu a aikin kai hari ga sansanin ƙungiyar boko haram a yankunan da suka bada da Parisu, Yale, Mongusu da kuma Kote, wanda yace ta cimma kyakkyawan nasara.

Oladele Yusuf ya ci gaba da cewa “yanzu kwarewarmu ta kai amatsayin sai mun bincike yanki da inda zamu kai hari kafin mu kai, sai mun lalata komai da komai na ‘yan bindigar kafin mu kai ga asalin kwaryar Sambisa” inji Oladele.

Ya bayyana aikin da rundunar ta gudanar cikin kashi biyu bisa ukun shekarar 2017 da cewa ta cimma muhimmiyar nasara bisa la’akari cimma mafuna da wargaza hari dama shirin ‘yan bindigar.

“manufar NAF shine samar da yanayi da rayuwa mai inganci ga fararen hula a yankin baki ɗaya, saboda haka muke gudanar da wasu ayyukan jinkai da suka shafi kiwon lafiya, kamar samar da magunguna da jinya kyauta ga ‘yan gudun hijira” inji shi.

Yace kuma sun samar da wata runduna mai ƙarfi a cikin garin Maiduguri da ciki da wajen jami’ar gwamnatin tarayya da ke birnin Maiduguri.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI