Connect with us

LABARAI

Sama Da ’Yan Arewa Miliyan 50 Ke Fama Da Talauci –Gwamna Shettima

Published

on


Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Shugaban gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu al’ummar arewacin Nijeriya sama da miliyan 50 ne ke kara-kaina a ƙarƙashin ƙangin talauci.

Shettima ya ƙara bayyana takaicin da dangane da wannan yanayi wanda yankin ya tsunduma a ciki, tare da nusar da cewa al’amarin ya fi ƙamari ɓangarorin ginshiƙan rayuwa guda biyar da suka haɗa da yadda jahilci yayi katutu ga zaman kashe wando, taɓarɓarewar sha’anin kiwon lafiya da sukurkucewar al’amurran kasuwanci da gudanar ayyukan bunƙasar tattali arziki da ɗabi’ar cima-kwance.

Kashim Shettima ya faɗi hakan ne a matsayin martani dangance da wasu alƙaluman sakamakon rahoton da masana suka fitar a yan kwanakin nan , wanda ya nuna cewa yan Nijeriya kimanin miliyan 79.6 ke fama da talauci, yayin da kaso 50 (daidai da kashi 70) daga cikin wannan adadin sun fito ne a tsakanin jihohin arewacin Nijeriya 19.

A bisa wannan dalili ne gwamnonin suka ƙulla wata yarjejeniya a Abuja da wata ƙungiya mai suna Memorandum of Understanding (MoU) domin kawo ɗauki a sha’anin kiwon lafiya da ya taɓarɓare jihohin arewacin Nijeriya baki ɗaya.

Hon Shettima ya tabbatar da cewa gwamnonin wannan yanki na arewa sun ƙuduri aniyar ɗaukar sahihan matakan sake bunƙasa fasalin rayuwar yankin a cikin ɓangarori da dama. Yayin nan kuma ya ƙara bayyana takaicin sa bisa ga ɗabi’un rashin kumari waɗanda suka yiwa yankin ƙawanya waɗanda kuma suka kasance silar halin koma baya da al’ummar ɓangaren ke fuskanta.

“Abubuwa ne waɗanda suke neman su sha ƙarfin mu, yayin da kuma dole ace mun lalubo hanya ƙwaya ɗaya wadda zata taimake mu wajen fita daga cikin wannan yanayin; hanyar kuma ita ce mu haɗa hannu da wannan hukuma ta General Electric, wadda ga dukkan alamu zata iya kaimu gaci domin bunƙasa tsare-tsaren kiwon lafiya a cikin waɗannan jihohi namu na arewa”. Inji shi.

“Akwai wasu rahotani waɗanda hukumar kula da lafiya ta majalisar ɗinkin duniya (WHO) ta taɓa bayarwa da a ciki ta tunasar da cewa akwai matsalolin da suka shafi mutuwar ƙananan yara da mata masu juna da dama a arewacin Nijeriya. Yayin da bisa ga wannan rahoton ne muka ɗauki wasu ingantattun matakai wajen ganin al’amurran sun ragu”. Ta bakin Shettima.

Gwamna Kashem ya ce ƙungiyar gwamnonin arewacin Nijeriya tana jin daɗin aiki da General Electric saboda a watan Oktoban 2015 hukumar ta taɓa cire miliyoyin dalili domin tallafawa yan gudun hijirar jihar Borno.

“Har wala yau, a cikin shekarar 2016 ƙungiyar gwamnonin arewa sun ƙulla makamanciyar irin wannan yarjejeniya da MOU domin girka tashoshin bayar da wuta mai amfani da hasken mai ƙarfin mega-wat 500 (Megawatts) da wasu jihohin arewa guda biyar.

“Yayin da a wannan karon kuma muke bukin ƙulla wata sabuwar yarjejeniya; a madadin sauran gwamnonin yankin arewa da MOU tare da hukumar General Electric domin farfaɗo da sha’anin kiwon lafiya a wannan yanki na arewacin Nijeriya”. Ya nanata


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI