Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

2019: Shekarau Ya Ayyana Takara A Ƙarƙashin PDP

Published

on


Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Yanzu haka dai a iya cewa ƙarshen tika-tika-tik a game da batun tsayawa takarar tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau a zaɓen 2019.

Ayyana cewa zai yi takara a zaɓen ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake na batunanin yiwuwar tsayawarsa zaɓen shugaban ƙasa ko a’a.

Malam Ibrahim Shekarau ya taɓa gwada sa’arsa inda Jam’iyyar ANPP ta tsayar da shi takarar zaɓen shugaban ƙasa wanda bai samu nasara ba.

Jawabin ayyana tsayawa takararsa ya fito da ga bakinsa a cikin wata takarda mai shafi biyu da aka raba wa ɗaukacin mutanen da ke cikin gwamnati lokacin da ya ke Gwamna a Kano, tsawon shekara takwas, da kuma abokan mu’amillarsa bayan zamansa Ministan Ilimi.

Takardar ta bayyana cewa, “Kamar yadda ku ka sani tun tsawon lokaci bayan kammala zaɓen shekara ta 2015, ana ta kiraye-kiraye daga al’umma da kuma ƙungiyoyi a faɗin ƙasar nan wanda ake nuna buƙatar na fito takarar kujerar shugabancin ƙasa a zaɓen shekara ta 2019. To ina da kyakkyawan zaton jama’a na yin haka ne sakamakon abubuwan da muka gudanar alokacin da muka jagoranci Jihar Kano a tsawon shekara takwas daga watan Yulin 2014 zuwa mayun shekara ta 2015”.

“Domin amsa kiran na al’umma tare da dogon tunani da kuma tuntuɓar  waɗanda ke da ruwa da tsaki cikin gudanar da wannan babban aiki, na tattauna da duk wanda ya kamata a shiyyoyin ƙasar nan baki ɗaya da kuma waɗanda suka nuna kishin abin alhairin da muka aiwatar a baya suka ba mu shawara ƙwarai da gaske.

“Saboda haka ina sanar da ku cewa sakamakon wannan tattaunawa da kuma tuntuɓa na aminta da wannan kira kuma na gamsu da cewa shiga a dama da mu cikin harkokin dimukuraɗiyya hidimtawa ƙasa ne wanda ya wuce maganar nasara a lokutan zaɓe. Saboda haka na yanke shawarar karɓar wannan buƙata ta al’ummar ƙasa, don haka za mu shiga cikin harkokin zaɓe tare da biyayya ga tsare tsaren Jam’iyyar mu ta PDP, don haka na miƙa kai domin tsayawa takara a zaɓen shekara ta 2019.

“Domin tabbatar da kyawawan ƙudurce-ƙudurcen Jam’iyyar PDP, ƙudirinmu da kuma aniyarmu ta yin wannan takara ya ta’allaƙa ne bisa tabbatar da ci gaban ƙasar mu Nijeriya, domin kare mutuncin ‘yan ƙasa da kuma mutunta ƙimar kowane addini ko ƙabila, ɗaukakarsu da kare buƙatunsu, sannan kuma za mu yi ƙoƙarin tabbatar da adalci a kowane mataki.

Har ila yau, Malam Shekarau ya ce za su yi ƙoƙarin ganin an kawo ci gaban tattalin arziki da ƙauna a tsakanin ‘yan ƙasa da kawo sauye-sauyen alhairi a tsakanin al’umma.

“Na rubuta wannan takarda domin sanar da ku cewar na yanke shawarar shiga wannan takarar shugabancin ƙasa a shekara ta 2019, sannan kuma ina neman gudanmawarku, shawarwari da kuma addu’ar ku, zan tabbatar da cewa a kowane lokaci a shirye na ke kuma ina maraba da duk wata shawara ko tsokaci kan wannan ƙudiri”, in ji takardar tshohon Gwamnan.

A halin yanzu dai za a iya cewa an kaɗa gangar siyasa duk da cewa Hukumar INEC ta gargaɗi ‘yan siyasa game da ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe tun lokaci bai yi ba.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI