Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Kafa Tarihin Lashe Kofin Gasar Uefa A Jere

Published

on


  • ‘Yan Madrid 13 Aka Gayyata Tawagar Kasashensu

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe kofin gasar zakarun kungiyoyin nahiyar Turai, bayan da ta samu nasarar kan takwararta ta Jubentus da kwallaye 4 – 1, a fafatawar da suka yi jiya a filin wasa da ke birnin Cardiff na Wales.

Wannan nasara da Madrid ta samu, yasa ta samu kafa tarihin zama kungiya ta farko, da ta lashe kofin sau biyu a jere, a gasar ta UEFA, zalika ta ci gaba da rike kambunta na zama kungiyar da ta fi lashe kofunan gasar ta zakarun kungiyoyin nahiyar turai, bayan da ta lashe kofi na 12 a jiya.

Dan wasa Critiano Ronaldo ne ya samu nasarar jefa kwallaye biyu, yayinda Casemiro ya jefa guda a ragar Jubentus.

Karo na biyar kenan, kungiyar Jubentus na samun nasarar zuwa wasan karshe a gasar ta cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai, amma bata samun nasarar lashe kofin.

Kimanin ‘yan kwallon Real Madrid 13 aka gayyata a tawagar kasashensu domin zuwa wasan sada zumunta da na gasar cin Kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

‘Yan kwallon da za su buga wa kasashen nasu tamaula sun hada da Barane da Carbajal da Ramos da Nacho da Isco da Morata da Asensio da Nabas da Modric da Kobacic da Cristiano Ronaldo da Pepe da kuma James.

Carbajal da Ramos da Nacho da Isco da Morata da kuma Asensio za su buga wa Spain a wasan sada zumunta da za ta yi da Colombia da wasan shiga gasar cin kofin duniya da Macedonia.

Shi kuwa Barane zai buga wa Faransa wasa biyu da za ta yi; wanda za ta ziyarci Sweden da kuma wanda za ta kece raini da Ingila.

Cristiano Ronaldo da kuma Pepe za su buga wa Portugal a wasan da za ta yi da Latbia, su kuwa Modric da Kobacic za su buga karawar da Croatia za ta ziyarci Iceland.

Keylor Nabas zai buga wa Costa Rica wasan shiga gasar cin kofin duniya da za ta kara da Panama da kuma wanda za ta yi da Trinidad da Tobago.

Yayin da James zai fafata a karawar da Colombia za ta ziyarci Spain da wadda za ta je Kamaru.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI