Connect with us

MANYAN LABARAI

RAHOTO: Kotu Ta Kori Karar Da Gwamnatin Jigawa Ta Kai Kwamishinonin Lamido

Published

on


Daga Munkaila T. Abdullah, Dutse

A ranar Litinin din makon da ya gabata ne, Kotun Cif majistare ta biyu da ke zamanta a Dutse ta kori karar da Gwamnatin Jihar Jigawa ta takai tsoffin kwamishinoni uku da suka yi mulki a lokacin tsohuwar Gwamnatin Sule Lamido.

Tsoffin kwamishinonin an gurfanar da su gaban kuliya a watan da ya gabata bisa zargin aikata laifuka hudu wadanda suka hada da almundahana, diban kudaden gwamnati ba bisa ka’ida ba, almubazzaranci da dukiyar al’umma wadda ya sabawa kundi na  97, 312, 123(A) da kuma sashi 287 na dokar jihar ta Jigawa.

Zaman kotun wadda mai sharia Ahmed Lamin ya jagoranta, ya bayyana cewa duk da cewar alkalin alkalai na jihar na da ikon maka duk wani mai laifi gaban kuliya, amma yafi dacewa ya shigar da karar a dunkule ba falle-falle ba.

“Don haka a yunkurin kotu na tabbatar da adalci ga kowanne bangare ba zata amince da cin zarafi ko batanci ga kowa ba”. A cewar hukuncin da aka zartar.

Alkali Lamin, nan take ya bayyana cewa kotu ta kori wannan kara gamida ba da umarnin sakin wadanda ake zargi da su tafiyarsu abinsu.

Bayan yanke wannan hukunci, lauyan masu kara BarristaMusa Muhammed Imam ya bayyana wa kotu kudurinsu na daukaka kara, yadda shi kuma lauyan wadanda ake zargi Barrista Yakubu Ruba suka yi na’am da wannan hukunci.

Tsoffin kwamishinonin dai sun hada da Alhaji Nasiru Umar da Alhaji Salisu Indirawa da kuma  Alhaji Abba Daguro.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI