Connect with us

BULALIYA

BULALIYA: Haramtacciyar Jamhuriyar Biyafara: Bukatar Ci Gaba Da Zama Hadaddiyar Kasa

Published

on


Tare da Al-Amin Ciroma 08033225331 (TES Kawai )   [email protected]       

Duk mai hankali da hangen nesa a nan kasar ba zai taba goyon bayan kabilar Ibo masu rajin ballewa daga Jamhuriyar Nijeriya su kafa tasu ba. Kamata ya yi a ce babbar kasa irin Nijeriya wadda ta yi fice a idanun duniya ta kowace fuska, ta wuce matsayin a rika ci gaba da ruruta wutar rikici ko yakin basasa.

Irin wannan yunkurin ya samo asali ne tu daga lokacin da Mista Nwankwo Kanu ya fara yekuwar sake farfado da haramtacciyar Jamhuriyar Biyafara. Hakan ta sa ya gamu da fushin hukumomi a Nijeriya, da har yanzu maganar ke kotu ana ci gaba da sauraren batu. Duk da ba zancen kotun za mu yi yanzu ba. A cikin ‘yan kwanakin nan kuma masu tada kayar bayan sun fara yada maganganu marasa tsari da hangen nesa, har suka tsayar da ranar 1 ga Oktoba 2017, ta kasance ranar da za su fara bayyana ballewarsu daga Nijeriya.

Kamar yadda muka sani, duk wanda ya san farkon rikici ko rigima, hakika bai san karshensu ba! Irin hakan ta sanya wata hadaddiyar kungiyar matasan Arewa, ita ma a nata bangaren ta fito da sanarwar bayan taron ‘yan jarida cewa, ta ba wa duk kabilar Ibo watanni uku ya fice daga Arewa. Jim kadan bayan da masu tada kayar bayan suka fito da ikirarinsu ne wasu kuma kungiyar sarakunan gargajiyar Kudu maso-Kudancin Nijeriya, ta fito da sanarwar musamman cewa ba ta tare da matasa masu yunkurin haddasa rikici da sunan kafa haramtacciyar Jamhuriyar Biyafara. Ba wannan kungiyar kadai ke yin tofin Allah-tsine ga masu rajin kafa haramtacciyar jamhuriyar ba, hatta wasu fitattun dattawan da suka shaida yadda yakin basasar 1967 ta kasance, su ma sun fito kwansu da kwarkwatarsu sun la’anci yunkurin.

A daidai lokacin da ya kamata ‘yan Nijeriya za su hada kai don kawo ci gaba a wannan zango da muka tsinci kanmu, ina amfanin kirkiro da matsalar da za ta iya haddasa koma-baya da asarar dukiya da rayukan al’umma? Idan har an aikata hakan, to wa zai gyara Nijeriya? Wa zai tabbatar da Nijeriya ta fita daga kangin da ta samu kanta a ciki?

Amsa a nan ita ce; Ni da kai za mu gyara Nijeriya! Kada fa mu manta, kafin zabukan 2015, idan ka yi tambayar ‘Wa Zai Gyara Nijeriya?’ Amsar da za ka samu ita ce; Baba Buhari ne zai gyara Nijeriya, alhali gyaran katafariyar kasa irin wannan ya fi karfin mutum daya.

Gabanin samun nasarar kafa gwamnatin canji, karkashin Shugaba Muhammadu Buhari, mafi yawan talakawa su na zaton da zarar an rantsar da Buhari, shi ke nan siddabarun canji zai game kowane lungu da sako na Nijeriya, alhali al’amarin ba haka yake ba. Shin ta yaya za a yi daudar da ta dankare a cikin jini da jijiyoyin kowane mahaluki a Nijeriya tsawon shekaru sama da sha-biyar su kau lokaci guda?

Kowa na son kasar nan ta gyaru, amma kowa kuma ya fallawa mutum daya ya gyara ta! Shin ta yaya za a yi Buhari shi kadai ya gyara tsarin bin doka da oda; Ya kiyaye cin hanci da rashawa; Ya dawo da martabar bin doka da oda; Ya cusawa ‘yan kasar baki dayansu akidar son Nijeriya; Ya yi nasa aikin ya yi na mutane sama da milyan 150? Shekaru nawa zai yi a gadon mulki?

Tilas mu dawo mu kalli kanunanmu, domin kuwa duk mai hankali ya san cewa Nijeriya ta shiga wani yanayi da babu wata kasa a duniya, mai wadannan dimbin albarkatu irin haka, amma ta samu kanta cikin tsaka mai wuya.

Da a ce ‘yan Nijeriya baki daya za su taru su yi wa kansu fada, sannan su gyara halayensu da kansu, shakka babu Nijeriya za ta ba wa kasashen duniya mamaki a cikin dan kankanin lokaci. Manazarta sun nuna cewa abu daya kawai ya kamata a ce ‘yan kasar nan sun runguma, wato bin doka da oda! Wannan kadai ya ishe mu. Matukar kowa zai dawo bisa turbar bin ka’idoji da dokokin kasa, shike nan an huta.

Ka dauki hanya daga gidanka zuwa kasuwa ko wani waje a cikin garin da kake, a nan ne za ka fahimci illar rashin bin doka da oda, da yadda gubar cutar ta yi mana katutu a zukatanmu. Za ka tarar babba ba ya tausayin na kasa da shi, shi kuwa karami ba ya ganin kima da darajar na gaba da shi. Ba mai saurarawa dan’uwansa sai rige-rigen karya dokar tuki. Kai, hatta matafiya a kasa, ba ruwansu! Hargowa kawai ake yi kamar an watso dabbobi bisa titi. Sannan duk da haka, kowa kuma yana son Buhari ya gyara Nijeriya. Ta wace hanyar zai fara? Shekaru nawa ake so ya wanzu a gadon mulkin Nijeriya kafin ya gyara dukkanin wadannan?

A yau Shugaba Buhari ya shafe shekaru biyu da kwanaki 11 cif a gadon mulkin Nijeriya, kenan kwanaki daga ranar 29 ga Mayun 2015 zuwa yau din nan 9 ga Yunin, 2017. Kwana nawa suka rage masa? Kwata-kwata abin da ya rage masa shekara daya da watanni 11 da kwanaki 19. Wanda ya yi daidai da kwanaki 718, sa’o’i 17,232, mintuna 1,033,920 da sakan 62,035,200.

Idan aka yi nazarin lissafin kwanakin nan da shugaban ya yi da wadanda suka rage masa a bisa mulkin Nijeriya, za a tabbatar da zancen da nake yi cewa ko da an kara ninka masa adadinsu, da wuya ya cimma nasara matukar ni da kai ba mu taimaka masa ba. Tun da ya hau mulki kawo i yanzu, zance daya kawai fa ake ta yi; wato badakalar sayen makamai. Ina batun almundahanar da aka tafka a hukumar matatar mai? Ina batun ma’aikatar sufuri? Ina batun miyagun gwamnonin da suka wawushe baitul-malin jihohinsu? Ina batun farfado da komadar tattalin arziki? Ina batun ba wa talakawa hakkinsu a dimokuradiyyance? Ina batun wadata kasa da abinci? Ina batun samar da ayyukan yi ga matasa domin rage fatara da yunwa?

Hakikanin gaskiya, kasar nan ba za ta iya fuskantar wani yunkurin ballewa ba, sannan ba za ta gyaru ba har sai ni da kai mun tabbatar wa kanmu gyara muke so, kuma da kanmu za mu yi. Ta wannan hanyar ne za mu iya taimakawa gwamnatin canji. Ta hakan ne kadai za mu iya kwace akalar shugabanci da ‘yan taratsin da ke kiran kansu shugabanni, alhali ko kawunansu ba su sani ba, balle su samu falsafa da ilmin tafiyar da mulki.

Mu lura da kyau, hatta tsarin manhajar karatunmu a Nijeriya suna bukatar garambawul. Kawo i yanzu babu wata jami’ar Nijeriya a cikin jerin fitattun jami’o’i 1000 na duniya. Ba don komai ba, sai domin mun bar shiri tun rani. Saboda haka muddin ni da kai ba mu bayar da gudunmawar tabbatar da sauyin kasar nan ba, wata rana Akuya za a kawo ta zama shugabar majalisar dattawa!

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI