WASANNI
Real Madrid Ta Koma Mataki Na Uku A Laliga

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta koma ta uku a teburin La Liga da maki 67 bayan da ta doke Malaga wadda take mataki na karshe har gida da ci 2-1 a ranar Lahadin data gabata.
A wasan na ranar Lahadi Real Madrid ta ajiye da dama daga cikin manyan ‘yan wasanta na yau da kullum da suka hada da Cristiano Ronaldo da Gareth Bale, bayan tsallake rijiya da baya da ta yi a gasar Zakarun Turai a hannun Jubentus da ci 4-3 jumulla.
Dan wasa Isco ne ya fara cin kwallo a minti na 29 inda ya zura kwallo a ragar tsohuwar kungiyar tasa, da wani kyakkyawan bugun-tazara.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 69 Isco din ya ba wa Casemiro kwallon daya zura ta biyu.
Ana dab da tashi bayan minti 90 na ka’ida Diego Rolan ya ci wa Malaga kwallo daya bayan kuskuren da Jesus Ballejo ya tafka.
Masu masaukin bakin wadanda wasan La Liga hudu kawai suka ci a bana, maki 14 ne tsakaninsu da tsira daga gasar yayin da ya rage wasa shida a kammala.
Real Madrid kuwa wadda ta wuce saman Balencia a tebur da wannan nasara, maki hudu ne tsakaninta da ta biyu Atletico Madrid, wadda ita kuma ta doke Lebante 3-0 a ranar Lahadin.
-
LABARAI9 hours ago
PDP Za Ta Kara Wa Mata Mukamai Idan Ta Lashe Zaben 2019 –Mariya Waziri
-
LABARAI9 hours ago
Fafutukar ’Yan NEPU Ce Ta Sa Talaka Ke Samun Mukami A Yau –Sule Lamido
-
LABARAI9 hours ago
2019: Kwankwasiyya Ta Raba Wa Mata 100 Naira 10,000 A Yobe
-
LABARAI9 hours ago
Mariri Ya Sha Alwashin Daukar Matasa Aiki
-
LABARAI9 hours ago
Dahiru Bauchi Ya Nemi Shugabanni Su Inganta Rayuwar Mutane Da Alheri
-
LABARAI9 hours ago
Sabon Katafaren Shago A Hajji Camp Zai Rage Wa Matasa Zaman Banza –Aminu Algazari
-
RA'AYI9 hours ago
Tambihi: Mutane 10 Da Za Su Bijirewa Buhari A 2019
-
LABARAI8 hours ago
Matasan Najeriya Ba Malalata Ba Ne –Fadila Tilo