RAHOTANNI
An Fara Garkuwa Da Kananan Yara A Giwa

A ranar juma’ar da ta gabata ne wasu mutane wadanda ba a San ko su waye ba suka sungumi wani yaro mai suna Aminu Yakubu dan shekara 7 a wata unguwa Madara a cikin garin Giwa ta jihar Kaduna.
Alhaji Yakubu shi ne uban yaron wanda ya ce, “ Wallahi ba zan iya cewa komai ba sai dai addu’ar Allah ya bayyana min wannan yaron” amma wani bawan Allah abokin uban yaron da aka sace, wanda ya ce a sakaya sunansa amma shi ma cewa ya yi “Tabbas a ranar Juma’a ne da misalin karfe 4 zuwa 5ny, Aminu ya fito yana wasa a kofar gidansu da ke unguwar ta Madara.
Kafin magariba sai iyayen Aminu suka lura bai shigo gida ba, sai aka fara nemansa tare da sanarwa ga duk inda ake sa ran ganinsa, amma babu labarinsa har zuwa wannan lokaci da muke wannan magana babu wani labari amma yanzu babu abin da muke yi illa rokon Allah ya bayyana mana wannan yaron”.
Ya zuwa yanzu bincike ya muna cewa, masu garkuwa ne suka shigo garin na Giwa inda suka sami sa’ar yin garkuwa da shi Aminu da wani yaro amma wancen yaron da suka tambaye shi cewa ina babanka? Sai ya ce musu “ Ai babana ya rasu” sai suka ce to mamanka fa? Sai ya ce “Ita ma ta mutu “ hakan ya sa suka sake shi amma sukaki Aminu.
Majiyarmu ta shaida mana cewa, masu garkuwar har sun kira wayar yayan Aminu tare da shaida masa cewa, sun yi garkuwa ne da Aminu har sai an ba su wasu miliyoyin kudi za su sako shi.
Wakilinmu tuntubi jami’an ‘yan sanda na garin Giwan don jin ko wane mataki suka dauka a kan lamarin.
DPO mai kula da wannan karamar hukumar bai samu damar cewa komai ba saboda alokacin suna tattaunawa kan maganar tsaro karamar hukumar.
Su ma kungiyar tsaro na Cibil Defence sun ki yarda su ce uffan, saboda al’amarin na gaban magabatansu.
Dakta Yahaya Ibrahim shi ne kantomar karamar hukumar ta Giwa wanda ya bayyana cewa, “A gaskiya ban ji dadin faruwar wannan lamari ba amma tuni na rubuta rahoto a kan lamarin na tura ga amma ina kira ga jama’ar karamar hukumata da su tashi tsaye wajan addu’a a kan wannan bala’i da ya shigo cikin kasa baki daya kuma za mu dauki duk matakan da suka dace wanda ba sai mun yada ba.
Saboda haka ina kira ga jama’a da su kula da yara tare da lura da duk wani bakon ido da ba a gane masa ba.
-
WASANNI17 hours ago
Ba Za Mu Dogara Da Ronaldo Ba A Wasanmu Da Bayern Munchen – Zidane
-
LABARAI17 hours ago
An Tsinci Sandar Majalisar Dattawa A Hanyar Maraba
-
WASANNI17 hours ago
Pogba Ya Raina Mourinho, In Ji Paul Scholes
-
LABARAI17 hours ago
Kafa Asusun Tallafa Wa Dalibai Daya Ne Daga Manyan Ayyukanmu –Sanata Kani
-
LABARAI16 hours ago
Za A Cigaba Da Daukar Malaman Firamare A Kaduna –Kwamishinan Ilimi
-
Madubin Rayuwa18 hours ago
Al’ummar Huli: Kabilar Da Maza Suka Fi Mata Iya Kwalliya
-
LABARAI17 hours ago
2019: Buhari Ya Cancanci Sake Tsaya Wa Takara –Sani Fema
-
LABARAI16 hours ago
Gwamnatin Yobe Ta Tura Dalibai 1,400 Karatu Waje –Gwamna Gaidam