Connect with us

ADABI

Martanin Sa’adatu Kankia: Ko Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu A Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya?

Published

on


Wannan wani martani ne da fitacciyar marubuciyar nan, MALAMA SA’ADATU SAMINU KANKIA, ta rubuta bayan kammala Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya da aka gudanar a birnin Katsina daga ranakun 16 zuwa 18 ga Maris, 2018, kuma ta aiko wa LEADERSHIP A YAU LAHADI. Ta rubuta martanin ne ga kasidar da mu ka wallafa a makon jiya mai taken ‘Katsina 2018: Ko Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu A Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya?’ wanda Yazid Nasudan ya wallafa. Ga dai ainihin abinda wannan Fasihiya Kankia ke cewa a cikin martanin nata:

 

Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu!

’Yan uwana marubuta barkanmu da wannan lokaci. Da fatan bakinmu na nesa da na kusa sun koma gida lafiya. Allah ya saka da alkairi ya bada ladar zumunci. Hakika wannan taron wani abu ne mai dumbin tarihi da ba za a manta da shi ba a tarihin marubuta. Taro ne da aka sha fama da gwagwarmaya da kalubale iri-iri kafin a samun tabbatuwarshi. To, sai dai Alhamdulillah! an yi taro lafiya an tashi lafiya.

Na karanta rubutun da Yazid Nasudan ya yi mai taken ‘Katsina 2018: Ko Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu A Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya?’. A cikin rahotansa ya fadi irin kalibalen da taron ya fuskanta, wanda a ciki ya ke cewa, ‘wani abun dubawa shi ne irin yadda taron ya yi shakulatin bangaro da jarumar da ta yi sanadiyar assasa taron tun farko, wato Fadila H. Aliyu Kurfi. Abin mamaki ne a ce ko a cikin takardar tsarin jadawalin taron sam babu sunanta kuma ko sau daya taron bai ambaci sunanta ba. Tabbas wannan babban butulci ne da babu wani abunda ya ke haddasa shi idan ba hassada ba. Kodayake dai Hausawa su kan ce ba a sauya wa tuwo suna. Saboda haka ko an ambaci sunan Fadila H. Aliyu Kurfi ko ba a ambace ta ba, ko an ba ta wata kulawa ko ba a ba ta ba, babu wani mahaluki da ya isa ya sauya tarihin cewa ita din dai ce ta yi sanadiyyar assasa wannan abin alheri da wasu su ke ta dagawa su na hura hanci da shi.’

Ko da ya ke Yazid ba marubuci ba ne kuma sanda mu ka fara tafiyar babu shi. A wannan karon Fadila ta kawo shi daga baya. Don haka ban san wannan maganar da ya fada mene ne hujjarsa ko a ina ya ji ko waye ya ba shi labari ba. Sai dai wani abu da na ke so duk wani marubuci ya sani shi ne tabbas Fadila ta yi kokari matuka wajen bude Gidan Marubutan Hausa tare da tattaro marubuta a duk inda su ke ta hada mu a cikin gidan. Tabbas ta yi kokari kuma ta cancanci a kira ta ‘jaruma!’

To, sai dai Ina so kowa ya sani cewa, Ni Sa’adatu Saminu Kankia ni ce na fara kawo shawara akan mu ma mu fara yin taron Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya a Gidan Marubuta na WhatsApp, saboda na je ofis din Aminu Ala na same su su na shirye-shiryen Ranar Mawaka a Bauchi. A cikin wadanda aka yi maganar akwai Zainab wouwo, Sister Iyami, Sadiya Garba Yakasai, Comd Zailani, Teemah Zaria da wasu da ba zan iya kawo su ba.

Amma a cikin wadanda na lissafa da yawansu su na cikin wannan tafiyar ta Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya da mu ka kammala, kuma na yi imanin su na sane da haka kuma za su iya bada shaida a kan hakan idan an tuntube su. Kuma a halin yanzu Ina tuntubar wasunmu da ba su canja waya ba su koma su dauko maganar duk da ta yi nisa, amma Ina sa ran za a iya samun ta kowa ya gani. An dade ana bi na ta ‘inbod’ ana cewa ‘yaya na bari ake ci da gumina? Don me ba zan fito na yi magana ba?’

A lokacin da mu ka yi wannan maganar, Fadila ma ba ta ‘online’, sai da ta zo ta tarar da shawarar da mu ka yi, sannan ne ta goyi baya. Daga nan muka hadu muka bada shawara akan cewa, Ado Ahmed Gidan Dabino ya jagoranci tafiyar.

An sha fama da shi kafin ya amince, saboda ya ce, harkar marubuta ba ta da dadi. A karshe muka sha kanshi ya yarda zai shige mana gaba. Daga nan ne aka fara shawarar ta yaya za a fara? Sai ya bada shawara akan cewa a yi zama na gemu-da-gemu, kuma nan take mu ka tsaida ranar da za a fara zama a ofis dinshi a Kano.

Aka fara tunanin abinda za a ci, idon an hadu, wanda ni din dai daga Kankia na dafa abinci na hada komai. Zainab Wowo ta taso daga Dutsinma ta zo muka tafi Kanon, yayin da Kabiru Assada ya bada 10,000 aka sayi lemu da ruwan da aka sha a wajen zaman ganawar. Kuma cikin ikon Allah aka tsaida matsaya akan shirya Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya Karo na Farko.

Abinda ya sanya na kawo wannan tarihin shine, saboda wadanda suka tarbi tafiyar a hanya, ba tare da su mota ta tashi ba tara su kayi suka hau, to gwanda a saka maganar a muhallinta. Kuma Ina kira ga masana da manazarta da su binciki wannan magana su gani.

Da wannan ne na ke yi ma kowa bankwana. Allah ya tabbatar ma na da alkairinsa, amin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai